Wahalar man fetur a Najeriya
Nigeria na fama da matsalolin da suka jefa 'yan kasar musamman talaka a cikin mawuyacin hali. Kadan daga matsalolin akwai lalacewar wuta, tsadar fetur da tsaro.
Wata tanka makare da iskar gas ta kife a jihar Katsina, inda ta aka ga wuta ya na tashi bayan fankar ta fashe tare da kamawa da wuta wanda ya jawo asara.
Kamfanin man fetur na kasa (NNPCL) ya ce Najeriya na samar da gangar danyen man fetur sama da ganga 1.8 a kullum kuma ana sa ran zai karu kafin karshen shekara.
Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), Nuhu Ribadu, ya yi magana kan amfanin cire tallafin man fetur da gwamnatin Bola Tinubu ta yi.
Kungiyar ƴan kasuwa masu zaman kansu IPMAN ta sanar da cewa za a samu saukin akalla N50 a farashin kowace lita idan ta fara ɗauko mai daga matatar Ɗangote.
Kamfanin mai na ƙasa, NNPCL ya ce tuni ya daina sayo tataccen man fetur daga ƙasashen ketare ya dawo kasuwanci da matatun mai na cikin gida a Najeriya.
Kungiyar IPMAN ta yi alkawarin karyewar farashin man fetur bayan ta yi yarjejeniya da matatar Dangote. IPMAN ta ce fetur mai rahusa zai wadata a Najeriya
A jihar Kano, hauhawar farashin man fetur ya sa mazauna garin canza hanyar sufuri. An ce yanzu sun koma tafiya a kasa, hawa kekuna ko amfani da babura masu lantarki.
Yayin da kamfanin NNPCL da ƴan kasuwa ke tsallake matatar Ɗangote, wasu kasashe takwas sun nuna sha'awar fara kasuwanci da mtatar attajirin ɗan kasuwar.
Wahalar man fetur a Najeriya
Samu kari