Wahalar man fetur a Najeriya
Yayin da ake ta ce-ce-ku-ce, rundunar sojojin Nigeriya ta bayyana dalilin tsare wani matashin dan jarida mai binciken kwa-kwaf, Fisayo Soyombo a Rivers.
Yayin da yan Najeriya ke cigaba da shan wahala saboda tsadar mai, Gwamnatin Tarayya ta kaddamar da motoci masu amfani da gas domin zirga-zirga kyauta a birnin Abuja.
Kungiyar dlillalan fetur ta fara nazarin farashin NNPCL. Kamfanin mai na kasa ya sanar da farashin fetur da za a sayar ga yan kasuwa daga matatar Fatakwal.
Hukumar kwastam za ta sayar da man fetur da araha a jihar Adamawa. Hakan na zuwa ne bayan kama man fetur ana shirin fita da shi daga Najeriya ta barauniyar hanya.
A wannan rahoton za ku ji cewa kungiyar Petroleum Products Retail Outlet Owners Association of Nigeria ta fadi matsayarta a kan labarin kara mata farashin fetur.
Kungiyar dillalan man fetur ta IPMAN ta bi jerin wasu daga cikin yan kasar nan wajen yin murna da gyara matatar mai ta Fatakwal, tare da fadin yadda za ta taimaka.
Kungiyar PETROAN ta ce farashin man fetur a matatar Fatakwal ya kai N1,045 wanda ya fi na Dangote tsada da. N75. Ana sa ran NNPCL zai daidaita farashin
'Yan kasuwar mai sun nuna farin cikin dawowar matatar Fatakwal inda suka ce akwai yiwuwar farashin fetur ya sauka saboda gasa da kuma wadatar man a kasuwa.
Gwamnati ta ce ana sa ran manyan motocin dakon mai guda 200 za su dinga loda fetur kullum daga matatar mai ta Fatakwal mai karfin tace ganga 600,000 kullum.
Wahalar man fetur a Najeriya
Samu kari