Wahalar man fetur a Najeriya
Rwanda ta gano danyen mai a karon farko a tafkin Kivu, tare da rijiyoyi 13. Najeriya da Angola na za su jagoranci samar da mai a Afirka da ganga miliyan 3.39 a rana.
Kungiyar IPMAN ta ce karin haraji daga NMDPRA ya janyo tsadar mai a kasuwa, inda farashin litar mai zai iya kaiwa N1,050 musamman ma a jihohin Arewa.
Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma ya ce cire tallafin man fetur rahama ce ga gwamnatocin jihohi saboda suna samun karin kudi domin gudanar ayyukan ci gaba.
Rahotanni sun bayyana cewa an samu karin farashin dauko mai daga rubunan ajiyarsu, wanda ya sa ake fargabar wannan zai jawo karin farashin fetur.
'Yan majalisar tarayya sun bukaci gwamnatin Bola Tinubu ta yi bayani kan kudin tallafin man fetur da aka ce an tara bayan cire tallafi. Minista ya gaza ba da amsa.
Rahoton Ofishin Mai Binciken Kudi na Kasa ya zargi hukumomin man fetur guda biyu na NUPRC da NMDPRA da rashin yin bayani a kan batan wasu biliyoyin Daloli.
Fitaccen lauya a Najeriya, Femi Falana ya ce marigayi tsohon shugaban kasa, Umaru Yar’Adua ya soke sayar da matatar mai ta Port Harcourt saboda rashin bin ka'ida.
Akwai yiwuwar a samu ragin farashin man fetur ya koma N500 saboda wasu tsarukan da ke tafe a gwamnatin Najeriya. Ana samun sauki a farashin man fetur.
Gwaman Babagana Zulum na jihar Borno zai siyarwa da manoma man fetur kan N600 duk lita domin rage mu su radadin da suke ciki na matsalar Boko Haram.
Wahalar man fetur a Najeriya
Samu kari