Labaran kasashen waje
An cafke tsohon shugaban Sri Lanka Ranil Wickremesinghe bisa zargin rashawa, bayan binciken ziyara zuwa London, inda ake zargin ya yi amfani da kuɗin gwamnati.
An tabbatar da rasuwar fitaccen alkalin nan mai tsantsar tausayin jama'a, Frank Caprio a ranar Laraba a kasar Amurka, ya mutu yana da shekaru 88 da haihuwa.
Kasar Iran ta bayyana cewa ba ta neman kowa da fada amma a shirye take ta aake fuskantar kasar Isra'ila matukar ta sake kawo mata hari, ta kera makamai.
Gwamna Bala Mohammed ya nada ɗan ƙasar China, Li Zhensheng matsayin mai ba shi shawa don jawo masu zuba jari, bunƙasa kasuwanci da gina ababen more rayuwa a Bauchi.
Sanatan kasar Colombia da ke da niyyar neman takarar shugaban lasar, Miguel Uribe Turbay ya mutu bayan shafe sama da watanni 2 yana jinyar harbin da aka masa.
Sanata Diket Plang ya zargi kungiyoyin waje da daukar nauyin hare-haren Bokkos, inda ya bukaci jami'an tsaro su tsaurara sa ido a kan iyakokin jihar Filato.
Gwamnatin Romania ya sanar da rasuwar tsohon shugaban ƙasar, Ion Iliescu, wanda ya mutu yana da shekaru 95 ranar Talata, za a shirya masa jana'iza ta ƙasa.
An yi gwanjon wata tsohuwar safa da mawaki Michael Jackson ya saka a 1997 kan Euro 6,200 a Faransa, duk da datti da tsufan da lu'ulu'un jikinta ya yi.
Jirgin sojin Venezuela ya fadi da ‘yan ƙabilar Yanomami a Amazon, kwanaki kafin hatsarin jirgi a Rasha da na Bangladesh, inda akalla mutane 300 suka mutu gaba ɗaya.
Labaran kasashen waje
Samu kari