Labaran kasashen waje
Larry Ellison ya zarce Elon Musk a arziki, inda yanzu ya zama mutum mafi arziki a duniya bayan darajar Oracle ta tashi da 40%. Yanzu dai Ellison ya mallaki N691.9trn
Matasa sun ce sun samu nasara a zanga zangar da suka kwashe kwana da kwanaki suna yi a Nepal bayan Firayim Minista, K.P Sharma Oli ya yi murabus a ranar Talata.
Kamfanin Apple ya ƙaddamar da sabbin wayoyin iPhone 17, inda zai fara sayar da su a Najeriya kan farashin ₦1.3m zuwa sama. Mun jero abubuwa 10 game da wayoyin.
Isra'ila ta tabbatar sa kai hari wani yanki a Doha, babban birnin kaaar Qatar da nufin kashe wasu shugabannin kungiyar Hamas da suka je tattaunawar zaman lafiya.
Wani rahoto ya nuna cewa Jamus, Ostiraliya, da Portugal sun zama wurare masu sauƙi kuma masu araha ga 'yan Najeriya da ke neman ƙaura, a maimakon Amurka da UK.
Masana kimiyyar Rasha sun sanar da kirkirar sabon maganin rigakafin cutar daji mai suna 'Enteromix,' wanda yanzu za a iya fara amfani da shi asibitoci.
Hukumar shige da fice ta Amurka ta kori 'yan Najeriya sama da 2,300 a cikin shekaru 11, inda aka sanya Najeriya a kan gaba a yawan 'yan Afirka da aka kora.
Sabuwar annobar cutar Ebola da ta bulla a DR Congo ta kashe mutane 15, WHO ta ce tana aiki cikin gaggawa tare da amfani da rigakafin Ervebo domin dakile cutar.
Shugaba Donald Trump ya karyata jita-jitar mutuwarsa da ta bazu a shafukan sada zumunta, ya ce bai taba jin wannan labarin ba sai da aka tambaye shi.
Labaran kasashen waje
Samu kari