Labaran kasashen waje
Harin ƙunar-bakin-wake a masallacin Shi'a dake Islamabad ya jawo mutuwar masallata 31 tare da jikkata 169; an auuama dokar ta-ɓaci a asibitocin Pakistan yau Juma'a.
Shugaba Bola Tinubu ya yi tafiye-tafiye 10 a 2025, yana jawo muhawara, yayin da Muhammadu Buhari ya yi tafiye-tafiye 21 a shekarar 2016 kacal a mulkinsa.
Binciken OCCRP ya bankaɗo yadda Nzube Ikeji ya damfari wata 'yar Romania $2.5m; ya yi ikirarin shi Yariman Dubai ne. An bankado yadda soyayyar intanet ta janyo zamba
Cikakken jerin kudaden kasashe 10 da suka fi daraja a duniya a 2026. Daga Dinarin Kuwait zuwa dalar Amurka, ga yadda darajar kudaden take a kasuwar canji.
Wani mai bara da ke kira Mangilal a kasar Indiya ya mallaki gidaje har guda uku, mota da abubuwan hawa masu taya uku da wasu makudan kudi a kasar Indiya.
Kasar Amurka ta gargadi yan kasarta kan ziyartar Nijar a 2026, saboda tabarbarewar tsaro da ayyukan ta’addanci, tare da sabbin sharuddan tafiye-tafiye.
Hukumomin kasar Colombia sun tabbatar da cewa duk mutanen da ke cikin jirgin Satena da ya bata jiya Laraba, sun mutu a hatsarin da ya rutsa da su.
Rahotanni sun bayyana cewa jirgin saman ya bata ne dab da zai sauka a yankim bodar Colombia da Venezuela, wanda yan tawaye ke da iko da shi, an fara bincike.
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya yi barazanar farmakar kasar Iran kan shirinta na nukiliya. Ya ce dole ne ta gaggauta zama nan teburin tattaunawa.
Labaran kasashen waje
Samu kari