Labaran kasashen waje
Ana ci gaba da musayar wuta tsakanin Iran, Amurka da Isra'ila, wannan matsala na iya yin tasiri da kawo tangarda ga ibadun musulumi a Ramadan, Umrah da Hajji.
Rahotanni daga Kudancin Lebanon sun nuna cewa Sheikh Hassan Ghandour ya rasu sakamakon raunukan da ya samu a hare-haren da Isra'ila ta kai har gidansa.
Biritaniya ta zargi Rasha da marawa Iran baya a yakin Amurka da Isra'ila. Minista Healey ya ce Putin na amfani da dabarun Ukraine don taimakon Iran.
Kasar China ta sanar da tallafin $200,000 ga iyalan daliban da aka kashe a harin makami a Iran, wanda Amurka da Isra’ila suka zargi da kai harin.
Sabon jagoran addinin Iran, Mojtaba Khamenei ya sha alwashin daukar fansar mahaifinsa da sauran wadanda suka yi shahada a yakin kasar da Amurka/Isra'ila.
Gwamnatin Isra'ila ta bayyana shakku karara a shirinta na kawo sauyin gwamnati a Jamhuriyar Musulunci ta Iran, ta ce har yanzu yan kasar na tare da ita.
Isra'ila ta hallaka kwamandan IRGC Abu Dharr Mohammadi a Beirut. Sojojin IDF na ganin kashe Mohammadi zai gurgunta ayyukan IRGC da Hezbollah a Lebanon.
Fitaccen mai watsa shirye shirye, Joe Rogan ya yi ikirarin cewa mafi yawa magoya bayan Shugaba Donald Trump sun fara tunanin ya ci amanrsu saboda yakin Iran.
Shugaba Donald Trump ya ce Amurka na iya ruguza wutar lantarkin Iran cikin sa'a guda amma tana kauce wa hakan. Ya ce sojin Iran sun raunata sosai yanzu.
Labaran kasashen waje
Samu kari