Yaki da ta'addanci a Najeriya
Karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle ya ga laifin masu cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ba shi da amfanin komai wajen ciyar da shiyyar Arewa gaba.
Wasu mutane dauke da manyan makamai sun kutsa kasuwar garin Faruruwa da ke karamar hukumar Shanono, inda suka hallaka wasu, tare da garkuwa da mutane.
Barista Audu Bulama Bukarti ya ce barin Boko Haram na mu'amala da mutane a TikTok ba karamar barazana ba ce. Ya ce ya kamata a rika rufe musu asusu.
Atiku Abubakar ya bukaci shugaba Bola Tinubu ya sanya dokar ta baci a kan mulkinsa saboda yawan kashe mutane da ake yi a Najeriya yana makale a kasar Faransa.
Rahotanni sun nuna cewa akalla gadoji biyu ƴan ta'addan Boko Haram ko ISWAP suka ruguza ta hanyar amfani da bama-bamai a jihar Borno da ke Arewacin Najeriya.
Mayakan kungiyar ta'addanci ta Boko Haram sun kai hare-hare a jihar Adamawa. 'Yan ta'addan sun hallaka mutane tare da tayar da bama-bamai a wasu kauyuka biyu.
Rundunar ƴan sanda ta Najeriya ta tabbatar da cewa ba za ta yi ƙasa a guiwa ba wajen kamo dukan masu hannu a kisan rayukan da aka yi a jihar Filato.
Fargaba ta karade al'ummar Otobi da ke a Benue bayan harin ba-zata da ‘yan bindiga suka kai, wanda ya tilasta jama’a tserewa daga gidajensu. An ji ta bakin ciyaman.
Mai alfarma sarkin Musulumi ya yi magana kan yadda ake kashe rayukan mutane a Najeriya musamman a Arewa a taron sarakunann Arewa na bakwai a Borno.
Yaki da ta'addanci a Najeriya
Samu kari