Wani Bom Ya Tarwatse da Mutane a Babbar Kasuwa a Najeriya, An Rasa Rayuka

Wani Bom Ya Tarwatse da Mutane a Babbar Kasuwa a Najeriya, An Rasa Rayuka

  • Rahotanni sun nuna cewa wani bom da miyagu suka dasa ya tarwatse a kasuwar Orlu da ke jihar Imo a Kudu maso Yamma
  • Jami'in hulɗa da jama'a na ƴan sandan jihar, Henry Okoye ya ce bom din ya tashi da masu ƙokarin dasa shi kuma sun mutu
  • Wata majiya ta ce mutane sun shiga tashin hankali bayan fashewar kuma akwai yiwuwar an rasa rayuka a sanadiyyar haka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Imo - Mutane sun shiga tashin hankali a kasuwar Orlu ta ƙasa da ƙasa da ke jihar Imo a lokacin da wani bom da aka dasa ya tarwatse yau Talata.

Rahotanni sun nuna cewa tashin bom din ya yi ajalin mutum biyu a kasuwar da ke Kudu maso gabashin Najeriya.

Kara karanta wannan

Bayan hukuncin kotu, an bayyana dalilin Tinubu na sakin yaran Kano da aka kama

Taswirar Imo.
Bom ya tashi a kasuwar Orlu, mutum 2 sun mutu a jihar Imo Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Yadda tashin bom ya hargitsa ƴan kasuwa

Fashewar bom ɗin ta haifar da turmutsutsu, inda jama'a suka fara gudun neman tsira wanda hakan ya sa da dama suka ji rauni, kamar yadda The Nation ta kawo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani mutumi da ya nemi a sakaya sunansa ya ce yana kasuwar lokacin da lamarin ya faru, mutane sun tsorata sosai, wasu sun fita hayyacinsu.

"Muna cikin kasuwar lokacin da muka ji ƙarar fashewar wani abu, an shiga tashin hankali da mutane suka fara gudun neman tsira, wasu sun mutu a tashin bom din," in ji shi.

An rasa rayuka a tashin bom?

Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sandan Imo, Henry Okoye, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce ƴan bindiga biyu sun bakunci lahira.

Kakakin ƴan sanda ya ce:

"Bom ne ya fashe kuma tuni kwamishinan ƴan sanda ya tura jami'an sashe kwance bom zuwa wurin. Mutum biyu da ake tunanin su suka sa bom din sun mutu a wurin."

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta yi magana kan yiwuwar dawo da tallafin man fetur a Najeriya

Okoye ya bukaci mazauna yankin su kwantar da hankulansu domin rundunar ta tura ƙarin dakarun ƴan sanda domin dakile duk wata barazana.

Yan sanda sun daƙile hari a Imo

Ku na da labarin jami'an rundunar ƴan sanda na reshen jihar Imo sun samu nasara a yaƙin da suke yi da ƴan ta'adda masu tayar da ƙayar baya.

Ƴan sanda sun daƙile wani harin ƴan ta'adda da ake zargin na ƙungiyar IPOB/ESN ne a ranar Talata, 29 ga watan Oktoban 2024.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262