Yaki da ta'addanci a Najeriya
Mafarauta da dama sun fada tarkon 'yan ta’addan Lakurawa a dajin Tangaza, inda ake fargabar 13 sun mutu. Sojoji sun dakile wani harin, amma an lalata turken MTN.
Sababbin hare-haren mabiya Bello Turji sun tilasta wa mazauna kauyuka 20 a Sakkwato yin hijira, yayin da matsalar tsaro ke ƙara ta'azzara a yankin.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya ce Najeriya ba za ta saduda, ta sunkuyawa masu yunkurin tayar da hankali ba, ya ce gwamnatinsa na inganta walwar sojoji.
Kasar Birtaniya ta yi magana kan tsohon sojanta da aka kama da Bindigogi a Najeriya. An kama mutumin da bindigogi kirar AK47 fiye da 50 a jihar Delta.
Kungiyar ISWAP ta dauki nauyin kai harin bam a Rann, jihar Borno, inda mutane 26 suka mutu ciki har da mata da yara; wasu sun yi konewar da ba a iya gane su.
Bam da aka dasa a hanyar Kala-Balge zuwa Gamboru ya hallaka matafiya 26, yayin da wasu uku suka jikkata. Gwamna Zulum ya yi kira da a kara tsaurara tsaro.
Gwamnatin Najeriya ta sha bayyana aikin da take yi wajen tabbatar da an samu tsaro a kasa, amma ba a cimma ruwa ba. Amnesty ta ce wannan halin bai yi ba.
'Yan ta'addan Boko Haram sun kai harin ta'addanci a Borno. Tsagerun sun hallaka mutane 12 ciki har da jami'an tsaro na 'yan sa-kai bayan sun yi musu kwanton bauna.
Rundunar sojin Najeriya ta kama wani dan bindiga da aka dade ana nema ido rufe mai suna Dogo a jihar Taraba. An kama wani mutum mai karya soja a Taraba.
Yaki da ta'addanci a Najeriya
Samu kari