Yaki da ta'addanci a Najeriya
Rundunar sojin Najeriya ta kai farmaki kan 'yan ta'adda a jihar Kogi. An kashe Kachalla Babangida bayan an bude wa 'yan bindiga wuta a wani dagi da suka buya.
Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta amince da gaggauta yin shari'ar dan Najeriya da ya kai hari ofishin majalisar dinkin duniya. An kama Khalid Al-Barnawi a 2016.
Rundunar ’yan sanda a jihar Anambra ta tabbatar da mutuwar mutane hudu tare da jikkata 15 a yayin harin yan bindiga da aka kai wajen masu zaman makoki.
A labarin nan, za a ji cewa gwamnatin Mai Mala Buni ta jihar Yobe ta bayyana takaicin yadda aka dawo da labarin kisan mutum 84 a Mafa a matsayin wanda ya faru yanzu.
Bayan cafke wasu daga cikin kwamandojin kungiyar Ansaru, Kotu da ke zamanta a birnin Abuja ta yanke hukunci kan Mahmud Usman, kwamandan Ansaru, hukuncin shekaru 15.
A labarin nan, za a ji cewa kasar Birtaniya ta sanar da cewa yanzu za a iya zuwa jihar Kaduna ba tare da katuwar fargaba a kan matsalar tsaro ba, kamar a da.
Binciken kwa-kwaf da aka gudanar ya karyata bidiyon da ake yadawa, inda ake ikirarin sojojin Najeriya na bai wa ’yan bindiga goyon baya a wani daji.
Sojojin Operation Fansan Yamma da jami’an tsaro sun yi nasarar dakile yunkurin ‘yan bindiga na kai hari wani kauyen karamar hukumar Malumfashi, an rasa rayuka.
Gwamna Nasir Idris zai kafa sansanin sojoji a karamar hukumar Augie, domin karfafa tsaro; ya kuma sanar da gyaran asibitin Augie don inganta kiwon lafiya.
Yaki da ta'addanci a Najeriya
Samu kari