Yaki da ta'addanci a Najeriya
Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa, ya jaddada cewa gwamnatin tarayya ba ta biyan kudin fansa ga masu garkuwa da mutane, duk da rade-radin jama’a.
Shugabannin al'umma a Sokoto Gabas na ƙorafi kan barazanar hare-hare daga Bello Turji, suna neman gaggawar taimako daga gwamnati bayan tserewar mazauna ƙauyuka.
Kakakin 'yan sanda Najeriya, Benjamin Hundeyin ya ce rundunar 'yan sanda ta kasa tana da bayanai a kan yadda Amurka ta kawo hari amma ba za su fitar da su ba.
'Yan sandan Katsina sun kama mutane 3 da sinadaran hada bama bamai 14,475 da na gelatine 2,273 a Daura; ana neman wani Najib da ake zargi da aiko da kayan daga Kano.
Gwamnan jihar Neja, Umaru Bago ya bukaci mutanen yankin Kaiji su kaura domin samun damar luguden wuta kan 'yan bindiga da ke kai hari. An ba su wata 2 su kaura.
Jami’ar Maiduguri (UNIMAID) ta musanta bidiyon da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke zargin kama dalibai bisa alaka da kungiyar Boko Haram a Borno.
Rahotanni sun nuna cewa kasurgumin dan bindigar nan, Bello Turji ya tura sakon barazana ga mazauna Tidibale, lamarin da ya sa suka fara guduwa a Sakkwato.
'Yan bindiga sun kai hari kan 'yan biki a Katsina, yayin da gwamnati ke kare shirin sakin 'yan bindiga a matsayin wani ɓangare na yarjejeniyar zaman lafiya.
Rahotanni sun tabbatar da cewa wasu miyagun 'yan bindiga sun mamayi jami'an tsaro yan sa-kai da kw sintiri, sun kai hari tare da kashe mutane 5 a jihar Benuwai.
Yaki da ta'addanci a Najeriya
Samu kari