Yaki da ta'addanci a Najeriya
A labarin nan, za s ji cewa maharan Boko Haram sun fitar da bidiyo cike da nuna raini da rashin kunya ga gwamnatin Najeriya bayan sace mutane a Borno.
'Yan bindiga sun kashe sojoji uku da ƴan banga a Kemanji, jihar Kwara, sannan suka sace motar yaƙi da makamai. Majiyoyi sun bayyana yadda maharan suka kai farmakin.
Fitaccen limamin coci a Najeriya, Bishof Oyedop ya ce nan da mako guda, fushin Allah da hukuncinsa zai fara afkawa yan binsiga da masu daukar nauyinsu.
Malamin Musulunci, Sheikh Ahmad Abubakar Gumi ya yi magana kan zuwan sojojin Turkiyya Najeriya, inda ya ce yana maraba da su domin magance rashin tsaro.
A labarin nan, za a ji cewa jam'iyyar ADC da ke hamayya da gwamnatin tarayya ta ce akwai babbar matsala a shirin dawo da ƴan ta'adda cikin jama'a.
Gwamnatocin Najeriya da Turkiyya za su kafa cibiyar horas da sojoji a Najeriya domin taimakon kasar ta magance matsalar tsaro da ta yi katutu a Najeriya.
Ana zargin cewa 'yan ta'addar Boko Haram sun kashe sojoji 4 da farar hula 1 a garin Mussa, Borno a ranar 15 ga Afrilu, 2026, yayin da sojoji suka dakile harin.
Rundunar sojojin Najeriya ta gudanar da jana'izar Janar da dakarunta da suka rasa rayukansu a hannun tsagerun 'yan ta'addan Boko Haram a jihar Borno.
Bincike ya nuna iƙirarin sojojin Amurka sun kama ƴan Najeriya 8 masu tallafa wa ta’addanci ƙarya ne. An gano Amurka ta sanya takunkumi kan mutane 8 ne kawai.
Yaki da ta'addanci a Najeriya
Samu kari