Yaki da ta'addanci a Najeriya
Rundunar yan sandan jihar Zamfara ta bayyana cewa dakarun hadin gwiwa sun tura yan bindiga 6 zuwa lahira a yankin karamar hukumar Maru ranar Talata.
A labarin nan, za a ji cewa rundunar sojin kasar nan ta aika dakaru zuwa jihar Zamfara bayan mazauna Zurmi sun rufe hanya saboda matsalolin tsaro a yankin.
Majalisar wakilan tarayya ta bukaci shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya dauki matakai masu tsauri domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin 'yan Najeriya.
Majiyoyi sun tabbatar da rasuwar Malam Yahaya Billi, shugaban Izala na Besse, bayan ya rasu a hannun masu garkuwa da mutane bayan fama da rashin lafiya.
Rundunar yan sandan jihar Zamfara ta yi nasarar hallaka 'yan bindiga uku da kama mutum a wani samame da suka kai cikin dajin Jangebe, sun kwato makamai.
A labarin nan, za a ji shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa, Opeyemi Bamidele, ya bayyana cewa nan gaba kadan za su amince da dokar kafa yan sandan jihohi.
Sanata Rabiu Kwankwaso ya bukaci gwamnatin Najeriya ta gaggauta daukar matakan da suka dace domin magance matsalar tsaron Najeriya da ya shafi jihohi da dama.
A labarin nan, za a ji shugabar daliban makaranta da aka sace a Oyo ta nemi a yi watsi da ikirarin gwamnati na cewa yan bindiga na neman a kafa Shari'ar Musulunci.
Tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi ya bukaci 'yan Najeriya su daina yi wa Fulani kudin goro game da ayyukan ta'addanci da garkuwa da mutane.
Yaki da ta'addanci a Najeriya
Samu kari