Yaki da ta'addanci a Najeriya
Zagazola Makama ya karyata rahoton cewa 'yan ta'addar Boko Haram sun kai hari a kauyen Kautikari da ke Chibok a jihar Borno inda suka kona wasu ajujuwan makaranta.
A labarin nan, za a ji cewa Boko Haram ta kai mummunan hari ƙaramar hukumar Chibok da ke jihar Borno inda aka kone wadansu makarantu a harin da ba a saba gani ba.
Ministan Tsaro a Najeriya, Christopher Musa, ya ce yaƙe-yaƙen Isra'ila da Iran da kuma na Rasha da Ukraine sun janyo ƙarancin kayan yaƙi a duniya.
Hedkwatar tsaron Najeriya ta bayyana alhininta kan rasuwar tsohon mai magana da yawunta, Manjo Janar Rabe Abubakar, wanda ya rasu a hannun yan bindiga.
Masu zanga-zanga kan tabarbrewar tsaron Najeriya sun sake fitowa a rana ta uku a Abuja, sun toshe titin Karu-Nyanya domin jawo hankalin gwamnatin tarayya.
Karamin ministan tsaro, Muhammad Bello Matawalle ya bayyana cewa yan adwa na amfani da halin da ake ciki na rashin tsaro wajen tunzura yan Najeriya.
Ministan tsaron Najeriya, Janar Chirstopher Musa (Mai ritaya) ya bukaci yan Najeriya su hada kai su taimaka wa jami'an tsaro don dawo da zaman lafiya.
Sanata Dino Melaye ya y kira ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sauka daga mukaminsa idan ba zai iya magance matsalar tsaro da ta addabi kasar ba.
Gwamnan Oyo, Seyi Makinde ya bayyana cewa bayanan sirri sun nuna cewa har yansu daliban da yan bindiga suka sace na nan a cikin gandun daji na Old Oyo National Park.
Yaki da ta'addanci a Najeriya
Samu kari