Gwamnatin tarayyar Najeriya
Sanatan Neja ta Gabas, Mohammed Sani Musa ya ce ba a fahimci abin da yake nufi ba kan cire tallafin mai, ya ce wasu mutane kalilan ke cinye kudin da ake warewa.
Tsohon shugaban marasa rinjaye na majalisar wakilai, ya bukaci Shugaba Bola Tinubu ya kara korar wasu minitoci. Dakta Wunmi Bewaji ya ce akwai sauran baragurbi.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da sake nada Farfesa Abdullahi Mustapha a matsayin Darakta Janar na hukumar NBRDA a wa'adi karo na biyu.
Kamfanin rarraba wutar lantarki a Najeriya watai TCN zai ɗauki akalla makonni uku yana gyaran wasu layukan wuta da aka gano suna yawan ba da matsala.
Saboda matsalar lantarki a Najeriya akwai, gwamnonin jihohin Gombe da Osun sun fara ƙoƙarin samar da lantarki domin rage dogaro da gwamnatin tarayya.
Masu cin gajiyar shirin N-Power na rukucin C II sun rubuta korafi ta hannun lauya, sun roki ministan jin kai, Nentawe Yilwatda ya biya su hakkin aikin da suka yi.
Gwamna Malam Uba Sani na jihar Kaduna ya maida kananaɓ yaran da aka sako bayan tsare su hannun iyayensu, ya ba kowane ɗaya N100,000 da wayar Itel.
Matasa masu yiwa ƙasa hidima wanda aka fi sani da NYSC sun ce har yanzun gwamnatin tarayya ta gaza cika alƙawarin karain alawaus zuwa N77,000 a wata.
Gwamnonin jihohin Arewa 19 sun yi ta'aziyyar rasuwar hafsan rundunar sojojin ƙasa, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja, wanda ya rasu bayan fama da jinya.
Gwamnatin tarayyar Najeriya
Samu kari