Gwamnatin tarayyar Najeriya
Tsohon shugaban kasa na mulkin soji, Janar Yakubu Gowon mao ritaya ya ce babu gurbin mulkin soji a Najeriya a yanzu, ya ba da shawara kan matsalar tsaro.
Gwamnatin tarayya za ta nuna wasu muhimman ayyukan da Bola Tinubu ya yi a birnin London. Ministan Abuja, Nyesom Wike na cikin jami'an da za su je taron.
Tinubu ya amince da kafa MediPool don rage farashin magunguna. Za a yi haɗin gwiwa da kamfanoni masu zaman kansu domin samar da ingantattun magunguna.
Gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ta tabbatar da batun biyan bashin Dala miliyan 3.4 da aka karɓi daga asusun bada lamuni IMF.
Jagora a APC, Dr. Mohammed Santuraki ya zargi gwamnatin tarayya da nuna bangaranci ga Neja a nadin shugabannin Hukumar Raya Arewa ta Tsakiya (NCDC).
Ministan harkokin Abuja, Nyesom Wike ya bayyana cewa ƴan Najeriya su ga canji a shekaru biyu da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi a kan karagar mulki.
Mataimakin shugaban ƙasa, Sanata Kashim Shettima ya jagoranci kaddamar da fara jigilar mahajjata daga Najeriya zuwa ƙasar Saudiyya, jirgin farko ya tashi a Imo.
Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa bai ɗauki matakai masu tsauri don jefa ƴan kasa cikin ƙunci ba sai don samun ci gaba mai ɗorewa a Najeriya.
Kungiyar ACF ta manyan Arewa ta buƙaci gwamnatin tarayya, gwamnatin jihohi da ta ƙananan hukumomi da jama'a su shiryawa zuwa ambaliyar ruwa a bana 2025.
Gwamnatin tarayyar Najeriya
Samu kari