Ma'aikatar Ilimin Najeriya
A farkon Watannan da muke ciki ne aka fara tafka muhara akan karatun jami'a a Najeriya, saidai shugaban jamb ya bayyana cewa ba dole bane sai kowa yaje jami'a
Wata jiha a Najeriya ta dauki wasu nakasassu aikin koyarwa a makarantun jihar. An bayyana cewa nakasassun kwararru ne kuma masu cancanta a fannin na koyarwa.
Gwamnatin jihar Borno ta shirya kafa kwalejin ilimin addinin musulunci guda 27 a dukkan kananaan hukumomi 27 dake fadin jihar don inganta karatun almajiranci.
Malaman firamare da a ka rage musu girma a Jihar Cross River, Calabar sunyi zanga-zangar rashin albashin na tsawon shekaru har shida bayan rage musu girma.
Gwamnatin tarayya ta shirya don tallafawa yaran da ba sa zuwa makaranta 10m a fadin kasar. Gwamnatin a karkashin shirin BESDA tuni ta fara gudanar da shirin.
Gwamnatin tarayya ta yadda a sake bude makarantu a fadin kasar baki daya. Gwamnatin ta bukaci makarantu da su kiyaye dokoki da ka'idojin kwayar cutar Korona.
Gwamnatin jihar Bauchi ta sanar da ranar 18 ga watan Junairu a matsayin ranar da zata bude dukkan makarantu mallakar jihar 4,816 tare da kiyaye dokar COVID-19.
Kungiyoyin jami'a na SSANU sa NASU sun fito zanga-zangar lumana don nuna kokensu kan wasu bukatunsu da suka gabatarwa gwamnatin tarayya amma ta gaga cika musu.
Wasu shugabannin jami'o'i sun bayyana shirinsu dabam domin dawowa makaranta. Sun ce sun shirya dasu da dalibansu kan bin duk wasu dokoki da ka'idojin COVID-19.
Ma'aikatar Ilimin Najeriya
Samu kari