Yan Majalisar Dattijai Sun Umarci Hukumar JAMB Ta Soke Amfani da NIN
- Majalisar dattijai ta umarci JAMB da ma'aikatar ilima su soke wajabcin amfani da NIN wajen yin rijista
- Majalisar tace kamata yayi hukumar NIMC ta nemo hanya mafi sauƙi da zata ba ɗaliban sakandire damar mallakar NIN a makarantunsu
- A wannan shekarar ne dai JAMB ta sanar da cewa ya zama wajibi kowane ɗalibi ya mallaki NIN idan yana son zana jarabawarta
A zaman majalisa na Talata, yan majalisar dattijai sun umarci hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire JAMB da ma'aikatar ilimi su soke wajabcin amfani da lambar NIN ko su ƙara lokacin yin rijista.
KARANTA ANAN: Da Ɗuminsa: IGP Ya Ƙaddamar da Rundunar ‘Operation Dawo da Zaman Lafiya Dole’ a Yankin Kudu
Majalisar ta umarce su da su sake duba shirin amfani da NIN ɗin a lokacin yin rijista, kamar yadda BBC ta ruwaito.
A wannan shekarar ne, hukumar JAMB ta maida amfani da NIN wajibi ga duk ɗalibin dake son zana jarabawar shiga manyan makarantu.
Sai dai a rahoton premium times, yan majalisar sun umarci JAMB da ta ƙara wa'adin yin rijista ko kuma ta soke amfani da NIN.
Wannan na ƙunshe ne a wani kudiri da Sanata Ifeanyi Ubah daga Jihar Anambra ya gabatar a gaban majalisar a zamanta na yau.
KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Yan Bindiga Su Hallaka Sojoji Biyu, Sun Yi Awon Gaba da Wani Ɗan China
Kudirin ya ƙunshi umarni ga ma'aikatar ilimi, hukumar samar da katin ɗan ƙasa (NIMC) da su nemo wata hanya da zata sauƙaƙa wa ɗalibai wajen samun lambar NIN a makarantunsu.
Kudirin ya kuma bayyana cewa dokar da JAMB tayi cewa wajibi ne kowane ɗalibi dake son zana jarabawa yayi amfani da lambar NIN ya saka ɗaliban cikin wahala.
A wani labarin kuma Ka Miƙa Kanka Ofishin Yan Sanda Dake Kusa, El-Rufa’i Ga Shugaban NLC
Gwamnan Kaduna , Malam Nasir El-Rufa'i yayi kira ga shugaban NLC ya miƙa kansa ofishin yan sanda mafi kusa dashi.
Gwamnan ya faɗi haka yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai jim kaɗan bayan kammala wani taro da ya halarta.
Asali: Legit.ng