Wata jiha a Najeriya ta dauki nakasassu 150 a aikin karantarwa

Wata jiha a Najeriya ta dauki nakasassu 150 a aikin karantarwa

- Gwamnatin jihar Oyo ta dauki sabbin malaman makaranta da suka kasance nakasassu

- Jihar, a kokarinta ganin ta dama da kowa a cikin al'umma ta bayyana daukar nakasassu 150

- Ana kuma sa ran nan gaba kadan za a ci gaba da daukar wasu a wasu ma'aikatu da ba na koyarwa ba

Gwamnatin Jihar Oyo a ranar Litinin ta ba da takardun daukar aikin koyarwa ga sabbin malamai 150 da aka dauka wadanda ke da nakasar jiki, Premium Times ta ruwaito.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa gabatar da takardun nadin an yi shi ne a katafaren ofishin sakateriyar Hukumar Koyar da Ilimi ta Jihar Oyo (TESCOM) dake Ibadan.

Alamu Akinade, shugaban TESCOM, wanda ya kula da gabatar da takardun, ya ce shirin ne makura na daukar ma’aikata 7,000 da suka kunshi ma’aikatan koyarwa da wadanda ba na koyarwa ba kamar yadda Gwamna Seyi Makinde ya amince da shi.

Mista Akinade ya bayyana nuna takardun a matsayin kawar shakku da korafe-korafen jama'a.

KU KARANTA: Yanzu yanzu: Hotunan bikin murnar yaye fursunoni 76 da suka kammala NCE na ta yawo a kafofin sada zumunta

Wata jiha a Najeriya ta dauki nakasassu 150 a aikin karantarwa
Wata jiha a Najeriya ta dauki nakasassu 150 a aikin karantarwa Hoto: The Sun Nigeria
Asali: UGC

“Idan akwai korafi kan wani nakasasshe da aka dauka; za mu janye takardun nan take.”

Shugaban TESCOM din ya kara bayyana cewa akwai kudurin daukar wasu nakasassun 50 a fannin da ba na koyarwa ba.

A nasa bangaren, mataimaki na musamman ga gwamna kan harkokin mulki Idowu Ogedengbe, ya ce tsarin daukar ma’aikatan ya dogara ne da cancanta.

Mista Ogedengbe ya ce duk da cewa an cire wasu nakasassu masu neman aikin daga gwajin na’ura mai kwakwalwa “amma mun yi gwaji ga dukkansu."

“Muna da kusan ayyuka 400 amma 330 ne suka bayyana a lokacin gwajin, yayin da 150 mafi kwarewa suka yi nasara.

Ayodele Adekanbi, Mashawarci na Musamman ga Gwamnan kan Nakasassu masu fama da nakasa, ya ce ana ci gaba da kokarin tabbatar da cewa wadanda aka dauka aikin sun kasance suna da kayan aikin koyarwa da suka dace da kuma yanayi mai kyau don sauke ayyukansu.

KU KARANTA: Jihar Sokoto ta kashe N740m akan rajistar WAEC da NECO na dalibai a jihar, in ji Tambuwal

A wani labarin, Mashahurin magana mai cewa shekaru ba komai bane face lambobi sun taka rawa a rayuwar 'yar Najeriya. Wannan lokacin game da neman ilimi ne, Hausawa dai sun ce gemu baya hana ilimi.

Matar da ke da shekaru 50 an gan ta a makarantar sakandare yayin da take zaune don daukar karatun.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.