Tirƙashi: Ba Dole Bane Ace Sai Kowa Yayi Jami'a, Inji Shugaban JAMB

Tirƙashi: Ba Dole Bane Ace Sai Kowa Yayi Jami'a, Inji Shugaban JAMB

- A wannan watan da muke ciki ne aka fara tafka wata muhawara akan Ilimin Jami'a a Najeriya

- Shugaban JAMB yace a nashi mahangar ba dole bane ace sai kowa yaje jami'a

- Shugaban ya bada misalai da cewa wasu zasu iya yin wani abu da yafi na masu jami'a muhimmanci

A farkon wannan wata na maris da muke ciki, dai anta tafka muhawara akan karatun jami'a a Nigeria, inda wasu suke ganin cewa ba dole bane.

Shugaban hukumar JAMB, Ishaq Oloyode, Shugaban kamfanin Bennie Technologies, Jerry Mallo, da kuma shahararren dan wasan kurme Tayo Osunkoya sun bayyana ra'ayoyin su dangane da wannan batu.

KARANTA ANAN: Kyakkyawan Mulkin da Buhari ya yi ne zai ba APC nasara a Zaɓen 2023, Inji Akpabio

Da aka tambayi Oloyede kan cewar ko yana ganin cewa karatun jami'a dole ne? Sai ya kada baki yace:

"Ya kamata ace dukanmu muje jami'a? Ina ganin amsar itace a'a. Wasu yaran zasu iya zuwa jami'a ya kasance basu amfana da karatun jami'ar ba, amma kuma ya kasance zasu iya yin wani abun wanda zaifi zuwan nasu jami'a mahimmanci."

"Yana dakyau a tsaya a duba tsarin dakyau. Yanzu kamar a kasar Ingila, zaka iya samun wanda yake harkar aikin haɗa hanyoyin ruwa ya kasance yana samun kuɗi kusan yadda farfesa ke samu ko ma ya fishi.

Baya da buƙatar ace dole sai yaje jami'a saboda tsari da yanayin da yake ciki ya bashi damar hakan." inji shugaban.

Tirƙashi: Ba Dole Bane Ace Sai Kowa Yayi Jami'a, Inji Shugaban JAMB
Tirƙashi: Ba Dole Bane Ace Sai Kowa Yayi Jami'a, Inji Shugaban JAMB Hoto: @JAMBHQ
Asali: Twitter

KARANTA ANAN: Abubuwa 4 masu muhimmanci da ya kamata ka yi idan wani ya turo kudi asusun bankinka cikin kuskure

A nashi ɓangaren, Jerry Mallo ya bayyana yadda ya zama shahararren mai ƙere-ƙere ba tare da mallakar kwalin digiri ba.

Ya bayyana yadda ya gaza samun damar zana jarabawar shiga jami'a, sannan zuwa sanda ya ajiye karatu zuwa kanikanci kafin daga bisani ya zamo shahararren mai ƙere-ƙere.

"Lokacin da sa'o'ina ke ƙoƙarin rubuta jarabawar shiga jami'a, ni kuma kawai sai na koma wajen kanikawa ina koyon irin aikin nasu saboda inaso in gano yadda injina suke aiki." A cewar shi.

"Nayi iya bakin ƙoƙarina a shekara ta ta farko a jami'a, amma da jarabawa ta fito, sai ya kasance sakamakon jarabawar baiyi kyau ba. Ranar kwana nayi ina kuka, inda daga nan ne kawai na yanke hukuncin ajiye karatun jami'a."

Osunkoya wanda ya kasance yana aiki a ɓangaren masu hada-hadar hannun jari, ya ajiye aikin nashi inda ya koma ɓangaren harkar wasannin kurme a cikin ruwa.

A cewarsa:

"Ban samu wata gamsuwa sosai ba akan abinda nake yi. A saboda haka ne a shekarar 1999 na yanke shawarar yin wani abu na musamman.

"Ban san wani wanda yake harkar kurmen ba, kuma babu wata makarantar koyon kurme a Najeriya. Amma dai kawai na sanya ma raina cewa akwai wani abu da nake son inyi," kamar yadda ya bayyana.

A wani labarin kuma Hukumar Hisbah ta wanke jami'inta da aka yiwa zargin kai matar aure Otal

Hukumar yan sanda ta kammala bincike kuma ta tabbatar ba shi da laifi. Jami'in ya shigar da wani gidan Rediyo kotu kan lamarin kuma ya nemi milyan 10

An damke Rimo ne a makonnin baya bayan rahoton cewa an kamashi da matar aure a Otal.

Ahmad Yusuf dan mutan katsinawa ma'aikacin legit.ng ne a bangaren Hausa. Ya fara aiki da legit kwa nan nan. Ahmad nada burin shahara a aikin jarida.

Kuna iya samunsa a kafar sada zumunta na twitter @ahmadyusufMuha77

Asali: Legit.ng

Online view pixel