Malaman firamare sun yi zanga-zangar rashin albashi na shekara 6

Malaman firamare sun yi zanga-zangar rashin albashi na shekara 6

Wasu malaman makarantar firamare a jihar Cross River sun yi zanga-zangar neman gwamnatin jihar ta basu hakkinsu

- Masu zanga-zangar sun bayyana cewa shekaru shida suka dauka ba tare da albashi ba

- A gefe guda SUBEB ta bayyana cewa tana kan bincika lamarin tuntuni

Malaman makarantar firamare na jihar Kuros Riba, wadanda Hukumar Ilimin Firamare ta Jihar ta rage darajar su a shekarar 2016, a ranar Laraba, sun yi zanga-zanga a Calabar kan rashin biyan su albashi na shekara shida.

Wasu daga cikin malaman, wadanda suka zanta da manema labarai a Calabar, sun ce SUBEB ta tsayar da albashinsu kuma wasu membobinsu sun mutu a cikin aikin, The Punch ta ruwaito.

Da take magana a madadin malaman, Misis Ekponwan Ekanem, ta ce, “Mun tsaya cak ne saboda ragin da aka yi. Sama da mu 2,000 ne abin ya shafa a duk fadin jihar.

KU KARANTA: Tsohon Ministan Wasanni Ka’oje ya mutu

Wasu malaman firamare sun yi zanga-zangar rashin albashi na shekara 6
Wasu malaman firamare sun yi zanga-zangar rashin albashi na shekara 6 Hoto: Business Day NG
Asali: UGC

“Ba a biya mu albashi ba tun shekarar 2016 kuma da yawa sun mutu saboda wahala. Wasu suna karbar kudin da ke ƙasa da albashinsu na wata yayin da wasunmu ma ba sa karɓar komai.

"Ba a kara mana girma ba kuma har yanzu muna ci gaba da koyarwa a yunwace."

Da yake mai da martani ga bukatun malaman, Sakataren SUBEB, Mista Cyril Itam, ya ce hukumar “tana jiran sakamakon rahoton binciken a kan lamarin daga ofishin Babban Odita Janar na Hukumar Kula da Karamar Hukumar."

“A watan Nuwamba na shekarar da ta gabata, mun kira duk wadanda suka gyara matsalolinsu da su zo kuma sun bi ta hanyar tantancewa don sanin halin da suke ciki a yanzu.

“Rahoton tantancewar yana tare da Odita Janar na Hukumar Kula da Ma’aikatun Kananan Hukumomi. Don haka, ana daidaita batutuwan.

"An sauke wasu zuwa mataki na 4 saboda ba su da cancantar koyarwa."

KU KARANTA: Garba Shehu yana goyon bayan masu aikata laifi -Ondo

A wani labarin, Gwamnatin Tarayya ta ba da amincewar sake komawa makarantu a ranar 18 ga Janairu bayan cimma yarjejeniya da Gwamnoni, Kwamishinoni da sauran masu ruwa da tsaki.

An cimma matsayar ne a wata ganawa tsakanin Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu da Kwamishinonin Ilimi a Abuja.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.