Gwamnatin Jihar Borno zata kafa kwalejin ilimin addinin Musulunci guda 27

Gwamnatin Jihar Borno zata kafa kwalejin ilimin addinin Musulunci guda 27

- Gwamnan jihar Borno ya yi kudurin kafa kwalejin ilimin addinin Musulunci a fadin jihar

- Gwamnan ya bayyana cewa zai kafa makarantun a kananan hukumomi 27 dake cikin jihar

- Manufar kafa makarantun shine bada hoto ga malamai don inganta karatun almajiranci

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, ya nuna shirin gwamnatin jihar na kafa kwalejin addinin Musulunci da ke ba da difloma a kowace karamar hukuma 27 da ke fadin jihar.

Gwamnan ya bayyana shirin ne a jiya yayin bude taron jin ra’ayoyin jama’a na kwanaki uku kan cikakken gyaran tsarin koyar da ilimin addinin Musulunci na gargajiya, This Day ta ruwaito.

Taron, wanda aka gudanar a babban dakin taro na gidan Gwamnatin jihar, ya tattaro adadin masu ruwa da tsaki wanda gudunmawarsu zai yi amfani wajen tsara tsarin aiwatar da tsarin koyar da ilimin addinin musulinci na gargajiya na Almajiranci.

Gwamnan, yayin da yake bayyana bude taron, ya ce gwamnatinsa na da shirin gina manyan kwalejojin Islamiyya guda 27; daya a kowace karamar hukuma 27.

KU KARANTA: Ku sabunta rajistarku da APC don ci gaba da zama a mukamanku, in ji Lalong

Jihar Borno zata kafa kwalejin addinin Musulunci guda 27
Jihar Borno zata kafa kwalejin addinin Musulunci guda 27 Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Manufar makarantar shine samar da dama ga manya wadanda suka cancanta da cikakkiyar ilimin addinin Islama su yi karatun difloma a fannin ilimin zamani domin inganta karantar da Almajirai a tsangayoyi.

Ya bayyana cewa za a tsara manyan makarantun Musuluncin don su ma su kasance cibiyoyin bincike na Musulunci baya ga koyarwa da koyo.

Wani Daraktan Cibiyar Ilimin Alkur'ani, na Jami'ar Ado Bayero da ke Kano, Farfesa Ibrahim Muhammad, wanda ya kasance bako mai jawabi a taron, ya jinjina wa Zulum saboda mayar da hankali kan salon shugabancin da ya kunshi cikakken shiri',

Ya kara da cewa: “Jihar Borno ta yi matukar sa’ar samun Zulum a matsayin shugabanta. ”

A cikin takardar tasa, Muhammad ya bayar da tarihi mai nuna yadda tsarin almajiranci ya fara a arewacin Najeriya, inda ya bukaci masu ruwa da tsaki a jihar da su ci gaba da mai da hankali kan shirye-shiryen da ake shirin yi.

KU KARANTA: Wata matashiya ta haifi tagwaye masu mabanbancin launin fata

A wani labarin, Gwamnatin jihar Borno ta nada Abba Umar Jato a matsayin Shehun Dikwa, Daily Trust ta ruwaito.

Abba Umar Jato ya gaji marigayi Shehu Mohammed Ibn Shehu Masta II El-Kanemi, wanda ya rasu a makon da ya gabata. Nadin nasa a matsayin mai fada aji na farko da Gwamna Babagana Zulum ya yi ya fito ne a cikin wata sanarwar da gwamnatin jihar ta fitar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel