Babu Wanda Zai Ci Nasara Fiye da Matakin Karatunsa, Shugaba Buhari

Babu Wanda Zai Ci Nasara Fiye da Matakin Karatunsa, Shugaba Buhari

  • Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya bayyana cewa babu wanda zai ci nasara fiye da ilimin da yake da shi
  • Buhari ya faɗi haka ne a wurin taro kan Ilimi na duniya dake gudana a birnin Landan
  • Shugaban yace yan Najeriya na sane da fifikon da ilimi ke da shi shiyasa suke sadaukarwa don baiwa yayansu ilimi

FCT Abuja:- Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, yace babu wani mutum da zai samu nasara fiye da ilimin karatun da yayi, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Buhari ya bayyana cewa duk mutunin da yayi wasa ya rasa ilimi to ya rasa komai na rayuwa.

Shugaban yace iyaye a Najeriya suna sadaukar da komai da suka mallaka domin tabbatar da 'ya'yansu sun samu ilimi.

Shugaba Buhari a Taron Ilimi na Duniya
Babu Wanda Zai Ci Nasara Fiye da Matakin Karatunsa, Shugaba Buhari Hoto: @BuhariSallau
Asali: Instagram

Buhari ya faɗi haka ne yayin wata tattaunawa ranar Alhamis a wajen taron ilimi na duniya dake gudana a birnin Landan.

Hadimin shugaba Buhari ta ɓangaren yaɗa labarai, Femi Adeshina, shine ya bayyana haka a wani jawabi mai taken "Yan Najeriya sun san ilimi yafi muhimmanci: Buhari ya faɗawa shugabannin duniya."

Shin Ilimi shine matakin cin Nasara?

Buhari yace yawan mutanen Najeriya wani ƙalubale ne ga kowace gwamnati, amma duk da haka yan Najeriya sun fahimci cewa Ilimi shine matakin farko na cin nasara.

Ya kara da cewa babu wani uba a Najeriya dake wasa da ilimi saboda sun san cewa idan yayansu ko yankin su ya rasa Ilimi to sun yi rashi babba.

A jawabin shugaba Buhari, yace:

"Ba zaka taba cin nasara fiye da matakin iliminka ba, duk wanda ya yi wasa ya rasa ilimi to tamkar ya rasa komai ne a rayuwa."
"Yan Najeriya sun baiwa ilimi fifiko, kuma iyaye suna sadaukar da kaomai nasu domin tabbatar da sun baiwa yayansu ilimi da yankin su."

An Gano ma'aikatan bogi a Bauchi

A wani labarin da muka kaeo muku na daban, Gwamnatin jihar Bauchi ta Gano Ma'aikatan Bogi 7,161 a Jiharsa, Ta Zare Su Daga Tsarin Albashi

A wani bincike da mataimakin gwamna ya jagoranta, Gwamnatin ta ɗauki matakin zare su daga tsarin baki ɗaya, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Ma'aikatan bogin sun kunshi waɗanda ke aiki da gwamnatin jiha da kuma na ƙananan hukumomi da kuma yan fansho.

Asali: Legit.ng

Online view pixel