Ku kula da yaranku, ba zamu iya tabbatar da tsaro a duk makarantu ba, gwamnati ga iyaye

Ku kula da yaranku, ba zamu iya tabbatar da tsaro a duk makarantu ba, gwamnati ga iyaye

-Hukumar ilimi a Najeriya ta shaidawa iyayen yara 'yan makaranta da su kula da 'ya'yansu

- Hukumar ta ce, ba lallai gwamnatin tarayya ta iya bai wa dukkan makarantu tsaro ba a yanzu

- An bukaci iyayen da su zama masu sanya ido a bangaren da ya shafi tsaro da kai rahoto ga jami'ai

Gwamnatin Tarayya ta jaddada bukatar ‘yan Najeriya da su yi taka tsan-tsan don kawo karshen hare-hare a makarantu da sace dalibai.

Karamin Ministan Ilimi, Chukwuemeka Nwajiuba, wanda ya bayyana hakan a cikin wata hira da jaridar The Punch a ranar Litinin, ya nuna cewa gwamnati ba za ta iya tabbatar da tsaron kowace makaranta a kasar ba.

A cewarsa, gwamnati ta umarci makarantu su kai rahoton duk wata barazanar tsaro ga hukumar tsaro mafi kusa.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Kotu Ta Raba Gardama Tsakanin FG da ASUU, Ta Yanke Hukunci Kan Yajin Aiki

A cikin tattaunawar, an tambayi ministan abin da gwamnati ke yi don kare makarantu daga hare-haren 'yan bindiga.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun budewa mafarauta wuta a Katsina, sun kashe 17, sun sace 25

Ku kula da yaranku, ba zamu iya tabbatar da tsaro a duk makarantu ba, gwamnati ga iyaye
Ku kula da yaranku, ba zamu iya tabbatar da tsaro a duk makarantu ba, gwamnati ga iyaye Hoto: Edufirst.ng
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya amsa da cewa, “Kulawa ta din-din-din itace farashin tsaro. Kowace kasa tana da damuwa a ko yaushe game da wayewar jama'arta.

"Gwamnatin Tarayya ba za ta iya tsare kowane gida ba. Kowa na bukatar yin ta kansa. Mun isar da wannan sakon ga dukkan makarantunmu ta yadda a duk inda suke, idan akwai wata barazana, to su sanar da hukumar tsaro da ke kusa da su.”

Nwajiuba ya kuma yi ikirarin cewa kusan duk makarantun kasar nan suna shinge. “Kusan dukkan makarantun da ke Najeriya, ko masu zaman kansu ne ko na Gwamnatin Tarayya, galibi duk suna da shinge, sai dai watakila wasu makarantun jihohi.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Wata cuta ta kama kama Nnamdi Kanu a hannun DSS, inji lauyansa

“Kamar yadda kuma ku ka sani, ko da kun sanya shinge, wadannan mutane ('yan bindiga) an san su da zuwa su kutsa ta kofofi.

“Don haka, shingen kewaye makarantu, da kansu, ba su da tasiri sosai. Matakin tsaro shine abinda ake bukata.

"Idan kun ji inda ake tsare da wasu daga cikinsu, za ku san cewa tambaya ce ta sanin kai da kuma al'ummomin da ke sanar da jami'ai a kan lokaci."

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya shawarci mata da su yi koyi da Ngozi Okonjo-Iwela

A wani labarin daban, Wasu daliban makarantar firamare uku da aka sace ‘yan awanni da suka gabata lokacin da wasu 'yan bindiga suka farma makarantar firamaren UBE da ke Rama a karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna sun tsere.

Da yake zantawa da daya daga cikin malaman makarantar, Daily Trust ta tattaro cewa tun farko an sace dalibai uku na firamare amma sun tsere lokacin da ‘yan bindigar suka yi kokarin satar wasu shanu da babura a wata unguwa da ke kusa.

Kara karanta wannan

Kungiyar 'yan China a Kano ta yi martani kan kisan da dan China ya yiwa budurwarsa a Kano

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.