Wasu jami'o'in Kotono 8 da dalibansu ba a amince su yi bautar kasa ba (NYSC)

Wasu jami'o'in Kotono 8 da dalibansu ba a amince su yi bautar kasa ba (NYSC)

- Hukumar NYSC a Najeriya ta bayyana cewa, ta barranta da wasu daidaikun jami'o'in waje

- A cewar hukumar, ba za ta bai wa daliban wasu jami'o'in Kotoni damar yin bautar kasa ba

- Sai dai, hukumar ba ta bayyana dalilanta, yayin da ake zargin saboda yayen dalibai jami'o'in ke yi cikin watanni ne dalili

Hukumar Kula da Matasa ta Kasa (NYSC), ta hana daliban da suka kammala karatu a jami’o’in kasashen waje guda takwas da ke Jamhuriyar Benin, Nijar da Kamaru daga shiga shirin bautar kasa na shekarar 2021.

An tattaro cewa jami'o'in, wadanda galibinsu suna bayar da digiri ne 'yan watanni kadan bayan shiga makarantun, ana kuma kiransu da "Jami'o'i Cotono".

A wata madauwari ta haramcin, mai dauke da kwanan wata 5 ga Maris, 2021, wanda aka jingina ga Kodinetan Jiha/Babban Birnin Tarayya kuma Daily Nigerian ta gani, ba a bayyana dalilin cire jami'o'in ba a hukumance.

KU KARANTA: Shehu Sani ya bayyana yadda 'yan bindiga suka kara zama abin tsoro a Kaduna

Wasu jami'o'in Kotono 8 da dalibansu ba a amince su yi bautar kasa ba (NYSC)
Wasu jami'o'in Kotono 8 da dalibansu ba a amince su yi bautar kasa ba (NYSC) Hoto: Daily Post
Asali: UGC

mma duk da haka ta umarci dukkan D&R da kuma jami’an da suka samu horo kan tantance jami'o'in kasashen waje da ke jihohi da su kula.

Cibiyoyin da abin ya shafa sune Al-Nahda International University (Nijar); Ecole Superieur Sainte Felicite (Benin); Ecole Superieur D Administration et DEconomics (Benin) da Ecole Superieur DEnseignement Professionelle Le Berger - ESEP Le Berger (Benin)

Sauran sun hada da Ecole Superieur St. Louis DAfrique (Benin); Superieur de Comm. Dord Et De Management - ISFOP (Benin) da International University, Bamenda (Kamaru).

Kwanan nan, Darakta Janar na NYSC, Shuaibu Ibrahim, ya zargi jami’o’i a Jamhuriyar Benin da gabatar da mutanen da ba su cancanta ba don yin aikin bautar kasa na shekara daya.

Mista Ibrahim, ya bayyana cewa NYSC ta fara gudanar da bincike kan ayyukan jami'o'in da ke da hannu a harkar zamba.

Hukumar bautar kasa ta matasa wani shiri ne da gwamnatin Najeriya ta kirkiro domin bunkasa hadin kai, shigar da daliban da suka kammala karatun su a sassan kasar da kuma ci gaban kasar.

KU KARANTA: Mijin Zahra Buhari ya nuna hotunansa tare da zakin da yake wasa dashi a gida, ya jawo cece-kuce

A wani labarin, Hukumar kula da matasa masu yi wa kasa hidiman ta kammala shirye-shirye don ba da allurar rigakafin Korona ta AstraZeneca, ga dubunnan mambobin bautan kasar na Batch A 2021 wadanda yanzu haka ke kan aikinsu a dukkan sansanoni 37 a fadin kasar.

An samu labarin cewa hukumomin NYSC sun hadu da kwamitin shugaban kasa kan Korona a Abuja don amincewa sannan za su kuma hadu da Hukumar Kiwon Lafiya a Matakin Farko, wani sashe na Ma’aikatar Kiwon Lafiya ta Tarayya kan shirin.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel