Ba Sauran Cece-Kuce: Majalisa Ta Amince Da Daidaita Kwalin HND Da Na Digiri

Ba Sauran Cece-Kuce: Majalisa Ta Amince Da Daidaita Kwalin HND Da Na Digiri

- Majalisar Dattawa karkashin jagorancin Ahmed Lawan ta amince da daidaita digiri da HND

- A yau Laraba ne majalisar ta tabbatar da amincewar bayan kammala zama na uku kan dokar

- Hakazalika Ahmed Lawan ya shawarci gwamnatoci da kamfanonin da su amince da dokar

Majalisar Dattawa ta amince da dokar da ta haramta nuna bambanci tsakanin babbar difiloma ta HND da kuma digiri na farko.

Lamarin ya biyo bayan kammala duba dokar a karo na uku da majalisar ta yi a yau Laraba, wanda kuma nan take ta amince da shi.

Sanata Ibrahim Shekarau daga Jihar Kano ne ya gabatar da rahoton kwamatin makarantun gaba da sakandare a zauren majalisar wanda ya duba Kudirin dokar mai suna 'Prohibition of Discrimination between First Degrees and Higher National Diplomas Bill, 2021 (SB.297)'.

KU KARANTA: Baya Ga Korona, Wata Sabuwar Cuta Ta Sake Bullowa a Kasar China Daga Kajin Gona

Ba Sauran Cece-Kuce: Majalisa Ta Amince Da Daidaita Kwalin HND Da Na Digiri
Ba Sauran Cece-Kuce: Majalisa Ta Amince Da Daidaita Kwalin HND Da Na Digiri Hoto: mrf.io
Asali: UGC

Shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawan ya ce batun nuna bambanci tsakanin babbar difilomar da kuma digiri ya fi shekara 15 a gaban majalisar.

"Wannan batun ya dade a gaban 'yan majalisa. Ina iya tunawa a Majalisar Wakilai ta 2003 zuwa 2007, wannan batun na cikin mafiya muhimmanci kuma wannan abin karfafa ne ga ɗaliban kwalejin fasaha (Polytechnic)," in ji shi.

Wannan na nufin kenan, daga yanzu babu bambanci tsakanin wadanda suka yi digiri a jami'a da kuma wadanda suka yi HND a kwalejin fasaha.

Sannan Ahmad Lawan ya roki gwamnatoci da kungiyoyi masu zaman kansu da su yi kokarin dabbaka sabuwar dokar.

"[Kuma] Ina rokon Gwamnatin Tarayya da dukkanin hukumomin gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu su fara aiwatar da wannan a lokacin da Shugaban kasa zai amince da wannan kudirin."

KU KARANTA: Gwamnan Zamfara Ya Tunkari Hedkwatar 'Yan Sanda Kan Dokar Harbe Masu Rike AK-47

A wani labarin, Shugaban majalisar wakilan Najeriya Femi Gbajabiamila ya ce kundin tsarin mulkin kasar na 1999 ya gaza magance wasu manyan matsaloli da ke addabar kasar, abin da ya sa kenan 'yan majalisa suka yanke shawarin sauya shi, BBC Hausa ta ruwaito.

Gbajabiamila ya fadi hakan ne a wajen taron jin ra'ayoyin jama'a kan sauya kundin tsarin mulkin a Legas a ranar Talata, kamar yadda wata sanarwa da mai bai wa majalisar wakilan shawara kan yada labarai ta fitar.

Shugaban majalisar ya ce kundin tsarin mulki ba wai tushen kasa ba ne kawai, kamata ya yi ya zayyana ka'idojin zaman kasa da kuma burikanta na akida da gaskiya, amma "namu kundin tsarin mulkin na cike da nakasu," a cewar Gbajabiamila.

Asali: Legit.ng

Online view pixel