Yanzu-yanzu: Gwamnati ta yadda a bude makarantu
- Gwamnati ta amince da bude makarantu ranar 18 ga watan Janairu
- Hakan ya fito ne daga bakin Babban Sakatare a Ma'aikatar Ilimi na Tarayya
- An bukaci makarantu da su kiyaye dokokin COVID-19
Gwamnatin Tarayya ta ba da amincewar sake komawa makarantu a ranar 18 ga Janairu bayan cimma yarjejeniya da Gwamnoni, Kwamishinoni da sauran masu ruwa da tsaki.
An cimma matsayar ne a wata ganawa tsakanin Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu da Kwamishinonin Ilimi a Abuja.
KU KARANTA: Hadarin hanyar Bauchi ya yi sanadiyyar rayukan mutane 21 daga cikin fasinjoji 22 - FRSC
Babban Sakatare a Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, Arc. Sonny Echono, wanda ya tabbatar da hakan ya ce:
“Mun tattauna sosai tare da gwamnonin jihohi, masu makarantu, kungiyoyin kwadago da na ma’aikata da wakilan daliban. Kuma yarjejeniya ita ce cewa ya kamata mu sake buɗe duk makarantu.
KU KARANTA: WHO ta dira Wuhan don bincike kan Korona
"Amma sake bude makarantun zai kasance cikin bin ka'idoji na COVID-19, musamman tsananin bin hanyoyin da ba magunguna."
Cikakkun bayanai jim kadan…
A wani labarin, Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya ya ce rufe makarantu saboda annobar COVID-19 zai yi tasiri mara kyau a kan ci gaba, aminci da kuma lafiyar yara a duniya, yana mai lura da cewa makarantu ba direbobin cutar ba ne, The Punch ta ruwaito.
UNICEF ta kuma yi gargadin cewa sakamakon rufe makaranta har shekara guda za a ji shi har zuwa tsara mai zuwa.
A wata sanarwa da hukumar ta fitar a ranar Talata ta ci gaba da cewa duk da kwararan shaidu da ke nuna cewa makarantu ba direbobi ne na cutar ba, an dauki matakai don tabbatar da cewa sun kasance a rufe.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng