FG Ta Ɗauki Nauyin Ɗaliban Kwalejin Afaka da Aka Sace, Zata Canza Musu Wurin Zama Na Wucin Gadi

FG Ta Ɗauki Nauyin Ɗaliban Kwalejin Afaka da Aka Sace, Zata Canza Musu Wurin Zama Na Wucin Gadi

- Gwamnatin tarayya ta gama shirin canza wa kwalejin FCFM wurin zama na wucin gadi biyo bayan sace ɗalibai da aka yi kwanakin baya a makarantar

- Gwamnatin ta kuma dauki nauyin biyawa ɗaliban da lamarin ya shafa kuɗin makaranta har su kammala karatun su

- Shugaban kwalejin FCFM Afaka, Dr. Usman M.B, shine ya bayyana haka a taron manema labarai ranar Litinin

Bayan garkuwa da ɗaliban kwalejin koyon zamanantar da aikin gandun daji FCFM, gwamnatin tarayya ta gama shirye-shiryen canzawa makarantar wurin zama daga Afaka zuwa wani wuri mai tsaro a cikin garin Kaduna.

KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Wasu Yan Bindiga Sun Sake Bankawa Ofishin INEC Wuta a Enugu

Hakanan gwamnatin ta sanar da cewa ta ɗauke wa ɗalibai 37 da aka sace kuma suka kuɓuta biyan kuɗin makaranta har su kammala karatunsu.

FG Ta Ɗauki Nauyin Ɗaliban Kwalejin Afaka da Aka Sace, Zata Canza Musu Wurin Zama Na Wucin Gadi
FG Ta Ɗauki Nauyin Ɗaliban Kwalejin Afaka da Aka Sace, Zata Canza Musu Wurin Zama Na Wucin Gadi Hoto: thenationonlineng.net
Asali: Twitter

Shugaban kwalejin, Dr. Usman M.B, shine ya bayyana haka ranar Litinin yayin da yake jawabi a taron manema labarai a kwalejin dake Afaka, ƙaramar hukumar Igabi, kamar yadda the nation ta ruwaito.

A jawabin shugaban kwalejin yace:

"Ministan muhalli, Dr. Muhammad Mahmood Abubakar, ya gama duk wani shirye-shirye na canza wa kwalejin wurin zama zuwa wani wuri mai tsaro a cikin Kaduna."

"Sannan za'a samar da motoci da zasu rinƙa jigilar ɗalibai da ma'aikata daga cikin makaranta zuwa inda suke buƙata a cikin garin Kaduna."

KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Kwamishinan Sokoto, Tureta, Ya Rigamu Gidan Gaskiya

"Hakanan kuma ministan ya bada umarnin a yafewa daliban da matsalar satar mutane ta shafa biyan kuɗin makaranta, saboda haka waɗanda ke karatun Difloma (ND) daga cikinsu, za'a ɗauke musu kuɗin ƙaratun babbar difloma (HND)."

Idan zaku iya tunawa legit.ng hausa ta kawo muku rahoton cewa, a ranar 11 ga watan Maris wasu yan bindiga suka kai hari kwalejin FCFM, inda suka yi awon gaba da dalibai 37.

Yan bindigan sun sako ɗaliban kashi-kashi, na ƙarshe da aka sako sune ɗalibai 27 a ranar 5 ga watan Mayu, bayan kwashe kwanaki 55 a hannun su.

A wani labarin kuma Bayan Ƙin Halartar Jana’izar COAS, Shugaba Buhari Yayi Magana da Matar Janar Attahiru a Waya

Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari, yayi magana da matar marigayi COAS Attahiru a waya tare da matan sauran jami'an da suka rasa ransu.

Buhari ya bayyana marigayi Ibrahim Attahiru da gwarzon soja wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen aiki ga ƙasar sa Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262