Babban kotun tarayya
PDP ta sake gamuwa da babbar matsala a jihar Ribas bayan kotu ta ba da umarnin dakatar da taron jam'iyyar da aka shirya gudanarwa a ranar 27 ga Yulin 2024.
Babbar kotun tarayya da ke zamanta a Legas a ranar Talata ta yi watsi da karar da wani lauya ya shigar na kalubalantar amfani da rubutun larabci a kan kudin Naira.
Gwamnatin jihar Kano ta maka tsohon kwamishinan kananan hukumomi, Murtrala Sule Garo, a gaban kotu. Ana zarginsa da sama da fadi da Naira biliyan 24.
Kotun daukaka kara da ke zamanta a birnin tarayya Abuja ta sanya ranar Laraba domin fara sauraron kararrakin da ke gabanta kan rikicin masarautar Kano.
Kotun daukaka kara ta tabbatar da nasarar da Gwamna Hope Uzodinma ya samu a zaben gwamnan jihar Imo. Ta yi watsi da karar da jam'iyyun adawa suka shigar.
Sabuwar dambarwa ta bullo a siyasar Kano bayan gwamnatin Abba Kabir Yusuf ya sake maka shugaban APC, Abdullahi Umar Ganduje a gaban kotu bisa zargin almubazzaranci.
Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde ya ce akwai rudani kan hukuncin da kotun tarayya ta yi kan yancin kananan hukumomi, ya kafa kwamiti domin duba hukuncin.
Wata babbar kotu dake Abuja, ta yi watsi da bukatar da tsohon gwamnan CBN Godwin Emefiele ya gabatar na neman izinin tafiya kasar Ingila (UK) domin neman magani.
Babbar kotun jiha da ke zamanta a Kano ta kawo karshen rikicin masarautar Kano, ta yanke hukunci a yau Litinin na haramtawa Sarki Ado Bayero bayyana kansa da sarki.
Babban kotun tarayya
Samu kari