Gwamnatin Najeriya
Gwamnatin tarayya ta sanar da cewa wasu masu zuba jari daga kasar Koriya ta Kudu za su gina matatun mai hudu da kowacce za ta iya tace ganga 100,000 a rana.
Gwamnatin tarayya ta ce matatar Dangote kadai aka amince ta rika samar da man jiragen sama ga kamfanonin jiragen saman kasar nan. Festus Keyamo ya yi bayani.
Gwamnatin tarayya karkashin shirin shugaban nasa na P-CNG, ta kaddamar da shafin da matasa za su nemi tallafin Keke-Napep 2,000 da za ta rabawa matasa.
Shugabar ma'aikatan Gwamnatin Tarayya, Didi Walson-Jack ta sake dawo da taken ma'aikatan Najeriya domin karawa musu kaimi a aikinsu na yau da kullum.
Hukumar sadarwa ta NCC ta sanar da cewa za ta hukunta attajirin duniya Elon Musk bayan kamfaninsa na Starlink ya kara kudaden da yake caja ba tare da izini ba.
Ministar al'adu da tattalin arzikin fikira a gwamnatin Tinubu, Hannatu Musa Musawa ta fito ta yi magana kan cece-kucen da ake yi kan batun cewa ba ta yi NYSC ba.
Tsohon Ministan sadarwa na kasa, Farfesa Isa Ali Pantami ya shawarci gwamnatin Najeriya da ta sake duba batun bayar da kariya ga shugabannin kasar nan.
Kamfanin man fetur na NNPCL ya ba yan kasuwa damar sayen man fetur daga matatar Dangote. Ana sa ran cewa hakan zai kawo saukin farashin man fetur a Najeriya.
Dan ta'adda Bello Turji ya yi karin haske kan neman sulhu da gwamnatin Najeriya da jihar Zamfara. Turji ya sake sabon bidiyo yana neman a kori yan sa kai.
Gwamnatin Najeriya
Samu kari