Gwamnatin Najeriya
Kungiyar gwamnonin Najeriya ta yi magana kan dakatar da gwamna Siminalayi Fubara da Bola Tinubu ya yi a makon da ya wuce. Sun fadi dalilin yin shiru kan lamarin.
Kungiyar matasan Ijaw ta maka Bola Tinubu a kotun ECOWAS kan dakatar da gwamna Siminalayi Fubara. An nemi kotu ta ci taran Tinubu dala miliyan 10 kan Fubara.
Babban lauya a kasar nan, Mike Ozekhome (SAN), ya zargi gwamnatin tarayya da karya dokar kasa, da kuma gudanar da juyin mulki a jihar Ribas, wanda ya saba doka.
Shugaban kwamitin amintattu na ALGON, Hon. Odunayo Alegbere, ya tabbatar da cewa gwamnatin tarayya ta na shirin fara biyansu kudadensu kai tsaye.
Gwamnatin Najeriya ta bayyana yadda ta yi amfani da diflomasiyya wajen kwashe jariran da ke da matsalar lafiya daga Gaza zuwa makotan kasashe kamar su UAE.
Wata 'yar Najeriya, Funke Iyanda na fuskantar hukuncin daurin shekaru 10 a Amurka kan zargin zamba da karɓar $40,980 daga tallafin rashin aikin yi ba bisa ka’ida ba.
Daya daga cikin manyan Neja Delta, Cif Anabs Sara-Igbe ya bayyana cewa fadar shugaban kasa ta dade ta na kitsa yadda za ta sanya dokar ta baci a Ribas.
Gwamnatin Najeriya za ta raba tallafin kudi ga manoma 250,000 a fadin Najeriya. Za a raba tallafin kudi da kayan aiki domin noman shinkafa, rogo da saransu.
Hadimin tsohon shugaban kasa, Reuben Abati ya bayyana fatan majalisar kasar nan za ta iya tsige Bola Ahmed Tinubu daga kujerarsa saboda karya dokar kasa.
Gwamnatin Najeriya
Samu kari