Gwamnatin Najeriya
Shugaban kungiyar yan ta'addan IPOB, Nnamdi Kanu ya amince da ya fara kare kan shi a gaban kotu. Ya lissafa gwamnoni, ministocin Buhari da Tinubu cikin shaidunsa.
Kungiyar malaman jami'a ta ASUU ta sanar da janye yajin aikin mako biyu da ta shiga domin gargadin gwamnati. Ta ba gwamnatin Tinubu wata daya ta biya bukatunta.
A labarin nan, za a ji cewa gwamnatin jihar Sakkwato ta bayyana yadda sabon tsarinta a kan sufuri ya taimaka matuka wajen dakile safarar yara daga jihar.
Mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima ya ba wata budurwa, Joy Ogah damar zama mataimakiyar shugaban kasa na rana daya. Ta yi magana kan ilimin mata.
Gwamnatin Najeriya tare da hadin gwiwar tarayyar Turai za su samar da guraben ayyuka 20,000 a Najeriya. Za a samar da ayyukan ne karkashin shirin NJFP 2.0.
A labarin nan, za a ji cewa kungiyar kwadago ta Najeriya, NLC ta ayyana shirin taya kungiyar malaman jami'o'i ta kasa, ASUU gagarumin yajin aiki a kasar na .
Kungiyoyin shiyyoyin a kasar nan sun yi Allah wadai da duk wani tunani da zai kai ga batun juyin mulki a Najeriya, suna cewa zai zama koma bayan gaske.
Gwamnan jihar Anambra, Charles Soludo ya yi magana kan masu neman ballewa daga Najeriya. Gwamnan ya yi magana kan masu neman a saki Nnamdi Kanu na IPOB.
Ana bincken tsohon gwama daga Kudancin Najeriya kan zarginsa da hannu a shirya wa shugaba Bola Ahmed Tinubu juyin mulki. An kama wasu sojoji kan lamarin.
Gwamnatin Najeriya
Samu kari