Gwamnatin Najeriya
Yayin da ake sa ran fara zanga-zangar gama gari a fadin Najeriya daga yau Alhamis 1-10 Agusta, 2024, wani lauya, Ebun Olu Adegboruwa ya nemi a rage kwanakin fita.
Gwamnatin tarayya ta bayyana fargabarta game da zanga-zangar gama gari da za a fara a ranar Alhamis, 1 Agusta, 2024, inda ta ce akwai rashin tsaro.
Kungiyar NADECO a kasar Amurka ta gargadi gwamnatin Najeriya kan taba masu zanga zangar adawa da tsadar rayuwa a Najeriya. Ta ce Tinubu ma ya yi zanga zanga a baya.
Sakataren gwamnatin tarayya, Sanata George Akume ya roƙi ƴan Najeriya su kauracewa zanga-zangar da aka shirya yi daga gobe Laraba, 1 ga watan Agusta, 2024.
Yayin da ake shirin fara zanga-zanga a gobe Alhamis, Kungiyar Take it Back Movement (TIB) a jihar Ogun ta bukaci Gwamna Dapo Abiodun ya samar musu da bas bas.
Fitaccen sarkin yarbawa Ooni na Ife ya yi kira ga ƴan Najeriya su kara hakuri domin tsadar rayuwar da suke kuka a kai ba a Najeriya kaɗai ake fama da ita ba.
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya roki 'yan kasar nan su marawa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu baya, inda ya ce shugaban na da kyawawan manufofi.
Akalla matasa 80,000 ne suka nemi tallafin Naira biliyan 110 awanni 72 bayan bude shafin asusun tallafawa matasa na NYIF. Jamila Bio Ibrahim ta sanar da hakan.
Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya ce gwamnati za ta rika biyan matasan Niger Delta Naira miliyan 500 duk wata domin bunkasa rayuwarsu karkashin NIS.
Gwamnatin Najeriya
Samu kari