Nade-naden gwamnati
Rahotanni sun bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu ya shirya korar shugaban ma’aikata, Femi Gbajabiamila tare da maye gurbinsa da tsohon minista, Babatunde Fashola.
Olukemi Iyantan ta zama kwamishiniya a hukumar NPC. Majalisar dattawa ta ce Iyatan ta cancanci nadin ne saboda kasancewarta a matsayinta na aikin gwamnati.
Bayan fadar shugaban kasa ta sanar da shirin Bola Tinubu na korar wasu Ministoci, yan siyasa da dama sun fara kama kafa tun bayan fitar da rahoton a Abuja.
Majalisar dattawan Najeriya ta tabbatar da naɗin Mai Shari'a Kudirat Kekere-Ekun a matsayin shugabar alƙalan Najeriya bayan bukatar shugaban ƙasa Bola Tinubu.
Fadar shugaban kasar ta kawo karshen jita-jitar da ake yadawa inda ta sanar da cewa Shugaba Bola Tinubu zai yiwa majalisar ministocinsa garambawul.
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya buƙaci majalisar dattawan Najeriya ta tabbatar da naɗin Mai shari'a Kidirat Kekere-Ekun a matsayin alkalin alƙalai CJN.
Allah ya karbi rayuwar Alhaji Abdullahi Sabi, mahaifi ga ministan ma'aikatar, Sanata Aliyu Sabi Abdullahi. An rahoto cewa ya rasu a ranar Litinin a Neja.
Daga dawowar shugaban kasa ya fuskanci matsalar ambaliyar ruwa, kudin fetur, zaben Edo da ASUU. Daga cikin bukatun da ASUU ke da su akwai biyan albashin malamanta.
Rahotanni da muke samu sun tabbatar da cewa hadimin Gwamna Umaru Dikko Radda na Katsina, Aminu Lawal Custom ya rasu a karamar hukumar Malumfashi.
Nade-naden gwamnati
Samu kari