Nade-naden gwamnati
An sallami Wale Edun da Ahmed Dangiwa sakamakon rashin lafiya da kuma gazawar fannin gidaje a wani gagarumin sauyin gwamnati a ranar 21 ga Afrilu, 2026.
Ahmed Musa Dangiwa ya miƙa godiya ga Shugaba Tinubu bisa damar da ya ba shi ta yin hidima ga ƙasa, jim kadan bayan an tsige shi daga mukamin ministan gidaje.
Shugaba Tinubu ya sallami Wale Edun da Ahmed Dangiwa tare da naɗa Taiwo Oyedele da Muttaqa Darma a matsayin sababbin ministoci a yau 21 ga Afrilu, 2026.
Shugaba Bola Tinubu ya sallami Wale Edun da Ahmed Dangiwa daga muƙaman ministoci a wani gagarumin sauyi da ya faru a yau Talata, 21 ga Afrilu, 2026.
A shafinsa na X, Salihu Tanko Yakasai ya yi rubutu da ya nuna yadda Bola Tinubu ya rasa goyon bayan Arewa sannu a hankali. Matashin ya ce ba a yi wa yankin adalci.
Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan na ci gaba da fuskantar matsin lamba daga bangarori daban-daban, ana neman ya sauka daga mukamin kafin zaben 2027.
Majalisar dokokin Kogi ta tantance tare da amincewa da tsohon shugaban APC na jihar, Abdullahi Bello, a matsayin kwamishina bayan bukatar Gwamna Ahmed Usman Ododo.
Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya sanar da rushe majalisar zartarwar jihar. Matakin na da da ya dauka zai fara aiki ne na take ba da bata lokaci ba.
Ministar kwadago, Nkeiruka Onyejeocha, ta yi murabus daga gwamnatin Tinubu a yau Juma'a, inda ta bayyana hakan a matsayin bude sabon babi na hidimar kasa.
Nade-naden gwamnati
Samu kari