Nade-naden gwamnati
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya amince da nadin Daniel Bwala wanda tsohon yaron Atiku Abubakar ne a matsayin hadiminsa na musamman a bangaren sadarwa.
Kamfanin mai na ƙasa watau NNPCL ya yi wasu ƴan gyare-gyare da nufin inganta ayyukansa da sauke nauyin da ya rataya a kansa, ya naɗa wasu a muƙamai.
Tsohon shugaban hukumar INEC, Attahiru Jega ya magantu kan yaduwar cin hanci da kuma halayen wasu yan Majalisar Tarayya wurin tilasta masu riƙe da mukamai.
Sabon gwamnan jihar Edo, Monday Okpebholo ya rusa shugabancin hukumomin gwamnati, ya sallami masu riƙe da muƙaman siyasa gaɓa ɗaya bayan shiga ofis.
Shugaban kamfanonin Tesla da X, Elon Musk ya samu muƙami a Amurka bayan amincewa da shugaban kasar mai jiran gado, Donald Trump ya yi da nadinsa.
Awannk kalilan bayan rantauwar kama aiki, sabon gwamnan jihar Edo, Monday Okpebholo ya naɗa sakataren gwamnati, akanta janar da kuma kwamishinan lafiya.
Tsohon Ministan wasanni da matasa, Solomon Dalung ya koka kan garambawul a gwamnatin Bola Tinubu inda ya ce ya kamata a sallami 70% na Ministoci.
Gwamnan Benuwai, Hyacinth Alia ya sanar da maido da antoni janar kuma kwamishinan shari'a kan kujerarsa bayan ya cika haruddan da aka gindaya masa.
Zababben gwamnan Edo, Monday Okpebholo, ya nada Fred Itua a matsayin Babban Sakataren Yada Labarai don inganta sadarwa tsakanin gwamnati da al’umma.
Nade-naden gwamnati
Samu kari