Aikin Gwamnatin Najeriya
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu na jagorantar taron FEC bayan makonni shida, SGF da shugaban ma'aikatan fadar gwamnatin Najeriya sun halarci zaman yau Talata.
Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya amince da naɗin Mr. Olatunji Bello a matsayin sabon babban jami'in hukumar FCCPC na ƙasa, ya masa fatan alheri.
Bayan shafe shekaru a tsare, shugaban haramtacciyar kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu ya zubar da makaman yaki inda ya bayyana cewa a shirye ya ke ya tattauna da gwamnati.
Bola Ahmed Tinubu ya ba Bisi Akande wanda amininsa ne mukami a gwamnatin tarayya da ya tashi rabon kujeru wannan karo a manyan makarantun gaba da sakandare.
Hukumar karbar korafe-korafe da yaki da rashawa ta jihar Kano ta bayyana kama wasu ma’aiakatan gwamnati guda biyu kan zargin sayar da takardun aiki ga mazauna jihar.
Jam'iyyar PDP a jihar Neja ta caccaki gwamnan jihar Umar Bago kan ziyarar da ya kai kasar Saudiyya tare da mataimakinsa da wasu manyan jami'an gwamnati.
Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya taya mazauna jihar murnar zagayowar ranar dimukuradiyya a Najeriya tare da bayanan halin da gwamnatinsa ta ke ciki.
Hukumar NASIMS ta fitar da sanarwa kan wadanda suka ci bashin Corona suka ki biyan kudin. Ta ce za fara cire kudi a asusun bankunan su har sai sun gama biya.
Bincike ya fallasa yadda gwamnatocin jihohin kasar nan 30 suka kashe makudan kudi wajen sayen kayan kwalam da makulashe da walwalar jami'an zaman gwamnati.
Aikin Gwamnatin Najeriya
Samu kari