"Duk da Masu Ja da Ikon Allah, Mun Yiwa Mutanen Kano Aiki," Gwamna Abba Gida Gida

"Duk da Masu Ja da Ikon Allah, Mun Yiwa Mutanen Kano Aiki," Gwamna Abba Gida Gida

  • Gwamnatin Kano ta bayyana cewa ta samu nasarori da dama cikin shekara guda a jihar duk da watanni takwas da aka shafe ana zaryar kotu kan kalubalantar nasararta
  • Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana haka a sakonsa na ranar dimukuradiyya ga al'ummar Kano da ya ce su ne suka jajirce wajen zabarsa, kuma ya na yi masu aiki
  • Daga ayyukan da gwamnan ya lissafa akwai biyan bashin 'yan fansho, aurar da zawarawa, sai daukar nauyin karatun dalibai a ciki da wajen Kano da raba tallafi ga masu sana'o'i

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya taya mazauna jihar murnar zagayowar ranar dimukuradiyya a Najeriya tare da bayanan halin da gwamnatinsa ta ke ciki shekara guda bayan zabarsa.

Kara karanta wannan

Majalisa ta fara binciken yawaitar hadurran jirgin kasa a Najeriya

Gwamnan ya ce duk da masu ja da ikon Allah da 'yan adawa suka so su yi ya kawo cikas a yanayin tafiyar da mulkin jihar, gwamnatinsa ta yi kokarin fara sauke nauyin jama'a.

Abba Kabir
Gwamnatin Kano ta bayyana nasarorin da ta samu cikin shekara guda Hoto: Sanusi Bature Dawakin Tofa
Asali: Facebook

A sanarwar da darakta janar kan yada labaran gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya wallafa a shafinsa na facebook, Abba ya ce zaman shari’ar kalubalantar mulkinsa ya shafe watanni takwas cikin shekara guda da ya yi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Mun samu gagarumar nasara,” Abba gida-gida

Gwamnatin jihar Kano ta ce cikin shekara guda da ya yi a kan mulki, an samu nasarori wajen yi wa al’umar Kano ayyuka a bangarorin koyar da kananan sana’o’i, ilimi da biyan bashin ‘yan fansho.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce an fara raba tallafin jari N50,000 duk wata ga mata 5,200 daga kananan hukumomin jihar 44, kuma an raba adadin kudin ga masu kananan sana’o’i a titi domin su kara jari, kamar yadda Kanofocus ta wallafa.

Kara karanta wannan

"An maida rai ba komai ba," Atiku ya riga shugaban kasa ta'aziyyar kisan Katsina

“Mun dauki nauyin karatu,” Abba

Gwamna Abba gida-gida ya ce sun dauki nauyin dalibai 1,001 da suka yi fice zuwa kasashen waje domin karo karatu a bangarori da dama.

Daliban da ke karatu a jami’o’in cikin gida kuma sun samu tallafin biyan wani kaso na kudin makarantarsu bayan kari da jami’o’in su ka yi a kwanakin baya.

Gwamnatin ta kuma kashe N2.9bn wajen biyan kudin jarrabawar kamala sakandare ta WAEC, NECO da NBAISda UTME, inji gwamnan.

Gwamnatin Abba da ‘yan fanshon Kano?

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa cikin shekara guda an samu damar biyan bashin da ‘yan fansho ke bin gwamnatin jihar tun a baya.

Ya ce an ware N11bn domin biyan ‘yan fansho 5,000 a tashin farko, kuma yanzu haka za a biya wasu a kashi na biyu hakkokinsu da ya kai N5bn.

Gwamnatin Kano ta kori yan kasuwa 5000

A wani labarin kun ji cewa gwamnatin jihar Kano ta umarci 'yan kasuwa masu shaguna a filin masallacin idi da su gaggauta tashi ko su fuskanci fushin hukuma.

Kara karanta wannan

Bayan APC ta samu galaba, gwamna ya rantsar da sababbin shugabanni 17

'Yan kasuwar sun ce sun shafe akalla shekaru 18 a shagunan da masarautar Kano da tsohuwar gwamnati ta mallaka masu, saboda haka suka roki gwamna ya duba lamarin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.