Aikin Gwamnatin Najeriya
A yanzu idan akwai wata kujerar da za a kira ‘ka fi minista’ a gwamnatin tarayya, Hadiza Bala Usman ce a kai. Ita ce ta ke da ta-cewa a kan makomar ministoci.
Gwamnatin tarayya da gamayyar kungiyar ma'aikatan Najeriya sun gaza cimma matsaya domin kawo karshen yajin aikin da ake yi saboda hana su albashin wata 4.
Wani bincike ya bankaɗo matsala a biyan albashin ma'aikatan kasar nan, inda ake fargabar samun jinkirin biyan kuɗin a watanni uku na Oktoba, Nuwamba da Disamba.
Wani lauya ya tono kuskuren Bola Tinubu wajen nada ministoci da ya yi karo na biyu bayan korar wasu ministoci. Lauya ya ce Tinubu ya karya doka kan nada ministoci.
Matan da za su zama ministoci a gwamnatin Bola Tinubu sun hada da Dr. Suwaiba Said Ahmad. Su ne sababbin matan da suka shiga gwamnatin APC mai mulki.
An kafa kwamiti da zai yi aiki a Majalisa ya yi bincike kan yadda aka dauki ayyuka a wasu hukumomi. Za a gabatar da rahoto a zauren majalisa cikin makonni hudu.
Tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo ya caccaki tsarin da Bola Tinubu ke bi wajen gudanar da gwamnatin kasar nan, inda ya zarge shi da rashin alkibla.
Jam'iyyun adawa sun ce korar ministoci da Bola Tinubu ya yi a banza ne, PDP ta ce korar ministoci kora kunya ne. LP ta ce Tinubu ya fara korar yunwa kafin ministoci.
Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya godewa mutum 5 da ya sallama daga matsayin ministoci tare da yi masu fatan alheri a duk harkokin da za su sa a gaba.
Aikin Gwamnatin Najeriya
Samu kari