Yan bindiga
An ceto ɗalibai mata guda 25 da aka sace daga makarantar mata da ke Maga da ke jihar Kebbi a Arewa maso Yammacin Najeriya bayan wasu biyu sun kubutua tun farko.
An shiga fargaba a Malumfashi bayan wani jami'in CJTF ya harbe Alhaji Ibrahim Nagode, mahaifin wani jagoran ’yan bindiga, har lahira. An ce DSS ta kama jami'an.
’Yan bindiga sun kai hari a Biresawa da wasu kauyuka a Tsanyawa, Kano, suka sace akalla mutum 8, ciki har da mata da matafiya. Mazauna sun tsere cikin dare.
Majiyoyi sun nuna hare-haren ’yan bindiga sun shafi aƙalla dalibai 2,496 cikin shekaru 11 a Najeriya tare da jawo tashe-tashen hankula musamman a Arewa.
Sheikh Ahamd Abubakar Gumi ya bayyana cewa ya fi damuwa a yi sulhu da yan bindiga fiye da ya tsaya wajen taimakon mutane da aka kawo wa hari, ya jero dalilai.
Shugaban cocin INRI Evangelical Spirirual, Primate Elijah Babatunde Ayodele, ya fito ya gayawa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu gaskiya kan rashin tsaro.
Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin sadarwa da dabaru, Bayo Onanuga, ya bayyana dalilin da ya sa sojoji ba za su iya yi wa 'yan bindiga rubdugu ba.
Mayakan 'yan Boko Haram sun kashe wasu mata bisa zargin su da yim amfani da laya a jihar Borno. An hango bidiyon da yan ta'addan suka wallafa a intanet.
An rufe makarantu da dama da ke a kan iyakar Abuja da jihar Niger saboda matsalar tsaro bayan sace dalibai a Niger da Kebbi. Malamai sun ce matakin na kariya ne.
Yan bindiga
Samu kari