Yan bindiga
Jami'an hukumar DSS sun kama wani dan bindiga da ya yi hijira daga jihar Zamfara zuwa Bauchi ya cigaba da rayuwa. An kama shi ne baya lura da yadda ya ke kashe kudi.
Amurka ta la’anci sace dalibai a Niger da Kebbi, tana kira ga gwamnatin Najeriya ta cafke masu laifi, ta kara tsaro, ta kare al’ummomin Kirista da sauran masu rauni.
'Yan ta'addan da ake zargi 'yan kungiyar Boko Haram ne sun sace mata 12 a jihar Borno. Rundunar 'yan sanda ta bayyana cewa tana kokarin ceto matan da aka sace.
Gwamnatin jihar Kaduna karkashin jagorancin Gwamna Uba Sani ta yi wa Nasir El-Rufai martani kan zargin ba 'yan bindiga makudan kudade har Naira biliyan daya.
Masu garkuwa da mutane sun kai hari a Toro, Bauchi, inda suka kashe dan agajin Izalah, Alhaji Muhammad Bakoshi, sannan suka sace matarsa da ‘yarsa mai shekara biyar.
Gwamnan jihar Neja, Umaru Bago, ya yi tsokaci kan matsalar rashin tsaro. Ya yi bayani kan rawar sa masu bada bayanai ke takawa wajen kai hare-hare.
Dalibai 50 daga makarantar St. Mary’s Papiri sun tsere daga hannun ’yan bindiga a Niger, yayin da daruruwan sauran dalibai da ma’aikata ke tsare a daji.
Yara sun fara barin FGGC Bwari bayan umarnin gwamnati na rufe makarantu 47 saboda barazanar tsaro da yawaitar sace dalibai a Arewa. Iyaye sun yi martani kan hakan.
Gwamnatin jihar Kebbi karkashin jagorancin Gwamna Nasir Idris ta yi wa Sanata Garba Maidoki martani. Ta zarge shi shi da yada bayanan karya kan rashin tsaro.
Yan bindiga
Samu kari