Yan bindiga
Gwamnatin jihar Neja ta tabbatar da cewa an yi nasarar hallaka yan bindiga 100 a kauyuka daban daban a karamar hukumar Shiroro, sai dai an rasa yan banga 14.
Shugaban kasa Bola Tinubu na tattaunawa da kasashen duniya domin shawo kan matsalar tsaron Najeriya. Jakadan Najeriya a majalisar dinkin duniya ne ya fadi haka.
'Yan bindiga dauke da makamai sun kai hari a jihar Imo. Tsagerun 'yan bindigan sun hallaka wani basarake tare da jami'an 'yan sanda yayin harin da suka kai.
Gwamnatin Tarayya ta fitar da jerin sunayen mutane da ƙungiyoyi 48 da aka ayyana a matsayin wadanda ke tallafa wa ayyukan ta'addanci a Najeriya na shekarar 2026.
Mazauna yankin karamar hukumar Shiroro a jihar Neja sun ce wadanda suka mutu a harin yan bindiga na ranar Talata sun hada da jami'an tsaro da fararen hula.
Gwamnatin jihar Bauchi ta tashi tsaye don dakile matsalar ayyukan 'yan bindiga. Gwamnatin ta rufe wasu kasuwanni da ake sayar da shanu a kananan hukumomi hudu.
Akalla mutane 24 sun mutu a harin Easter a Kebbi a kauyen Debe, yayin da maharan suka kona coci da masallaci, abin da ya kara nuna tsananin tabarbarewar tsaro.
'Yan bindiga dauke da makamai sun kai harin ta'addanci a jihar Plateau. Tsagerun 'yan bindiga sun kashe mutanen da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba.
Kungiyar Boko Haram ta saki bidiyon wasu mutane da ta kama a garin Ngoshe da ke jihar Borno. Mutan da aka sace sun nemi taimakon gwamnatin Najeriya.
Yan bindiga
Samu kari