Yan bindiga
Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya yabawa dakarun sojojin Najeriya bisa nasarar da suka samu ta hallaka wani gawurtaccen shugaban 'yan bindiga.
Wasu 'yan bindiga da ake ganin masu garkuwa da mutane ne sun yi savuwar aika-aika a jihar Legas. 'Yan bindigan sun sace manajan darakta na kamfani.
Gwamnan Zamfara ya ce sai a kama ‘yan bindiga, amma alkali ya ba da belinsu a kotu. Dauda Lawal Dare ya tabbatar da cewa matsalar rashin tsaro ya fi karfinsa.
Gwamnatin jihar Katsina ta bayar da kyautar Naira miliyan 6 ga iyalan ‘yan sanda hudu tare da wasu jami’an tsaro uku na jihar wadanda ‘yan bindiga suka kashe su.
Rundunar ‘yan sandan kasar nan ta bayyana samun nasara kan wasu miyagu da ke taimakawa ‘yan ta’adda su na muzgunawa al’umaar kasar nan a babban birnin tarayya Abuja.
Sojojin Najeriya sun kai tagwayen farmaki kan 'yan ta'adda a jihohin Abia da Ondo a kudancin Najeriya. Farmakin ya jawo lalata sansanin 'yan ta'addan IPOB da ESAN.
Dakarun sojojin Najeriya masu aikin wanzar da zaman lafiya sun samu nasarar hallaka wani gawurtaccen shugaban 'yan bindiga da mayakansa yayin wani artabu a Kaduna.
Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya koka kan cewa ba shi da iko kan harkokin tsaro a jihar. Gwamnan ya bayyana abin da ke kawo cikas wajen magance 'yan bindiga.
Wasu miyagun 'yan bindiga sun tare hanyar Kaduna zuwa Abuja inda suka yi awon gaba da fasinjoji masu yawa. 'Yan bindigan sun yi ta'asar ne a cikin dare.
Yan bindiga
Samu kari