Yan bindiga
yan sanda a jihar Akwa Ibom sun kashe yan bindiga uku cikin wadanda suka sace daraktan ma'aikatar shari'a suka daure shi a cikin wani rami da 'yar uwarsa.
Yan sanda a Katsina sun kama wani rikakken dan damfara da ke satar ATM yana cire kudin mutane. An kama matashin da ya sace matar aure a jihar Katsina.
Yan ta'adda sun dasa bama-bamai a garin Dansadau da ke karamar hukumar Maru a Zamfara inda yan sanda suka zargi kungiyar Lakurawa da alhakin kai harin.
Rundunar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Zamfara ta zargi sabuwar kungiyar 'yan ta'addan Lakurawa da alhaki wajen dasa bama-bamai a wasu kauyukan jihar.
Mutane 12 sun mutu a Yar Tasha, Zamfara, bayan motar haya ta taka wani abin fashewa. An nemi gwamnati ta dauki mataki don dakatar da wannan barazanar.
Yan bindiga masu garkuwa da mutane sun sace kansila da wasu mutane 8 a jihar Kogi. Yan bindigar sun bi gida gida ne suna garkuwa da mutane a yankin.
Wasu 'yan bindiga sun tare hanya tare da yin garkuwa da wani limamin cocin Katolika a jihar Enugu. An fara kira ga jama'a da su yi adduo'i domin ganin ya kubuta.
Rundunar yan sanda ta kama gagararrun yan bindiga yayin da ta kai hari wata maboyar 'yan ta'addar IPOB da ESN a jihar Imo bayan daukar lokaci tana samame.
'Yan bindiga sun kashe fasto a Kwara yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa jana'iza. Sun yi garkuwa da wasu mutum uku kuma suna neman Naira miliyan 30 kudin fansa.
Yan bindiga
Samu kari