Yan bindiga
Gwamnatin jihar Niger ta dakatar da hakar ma'adanai a fadin jihar kuma ta umarci hukumomin tsaro da su rubuto mata bayanai kan dukkan wurin hakar ma'adanai.
Wasu yan bindiga da ake zaton masu garkuwa ne sun sace Yariman ƙauyen Bari da ke ƙaramar hukumar Rogo a jihar Kano, tare da wata matar aure a ranar Talata.
An kashe wani mai gadi mai suna Sunday a gidan man Titolu Venture da ke Igoba a karamar hukumar Akure ta Arewa a jihar Ondo a Kudu maso Yammacin Najeriya..
Dakarun Operation Safe Haven sun dakile yi nasarar dakile wani hari da yan bindiga suka kai garin Gajin Bashar da ke karamar hukumar Wase ta jihar Plateau.
Wani dan bindiga ya bude wuta a yau Litinin a wani faretin bikin ranar ‘yancin kai na Amurka a jihar Illinois, inda ya kashe akalla mutane shida a yayin faretin
Wasu yan bindiga da ake zaton masu fashi da makami ne sun kaddamar da hare-hare kan manoma a yankin gabashin jihar Sokoto. Sun kashe manoma 11 a gonakinsu.
Yan ta'adda a sa'o'in farko na ranar Litinin sun sake yin garkuwa sa wani limamin cocin katolika, Rabaren Fada Emmanuel Silas a karamar hukumar Kauru ta jihar.
Wasu tsagerun yan bindiga da ake zaton masu garkuwa da mutane ne sun yi awon gaba da wasu limaman cocin Katolika biyu a jihar Edo a ranar Asabar, 2 ga Yuli.
Tsagerun yan bindiga sun farmaki garin Angwan Baraya da ke masarautar Pyem, karamar hukumar Mangu ta jihar Plateau inda suke ta harbi kan mai uwa da wahabi.
Yan bindiga
Samu kari