Yan bindiga
Wani jirgin yaki ya saki boma kauyukan Gidan Sama da Rumtuwa a karamar hukumar Silame bisa kuskure. Jirgin ya saki bom din ne yana kokarin kashe Lakurawa.
Rundunar 'yan sanda sun yi kare jini biri jini da 'yan bindiga a jihar Imo. An kashe 'yan sanda biyu yayin da aka kashe yan bindiga uku aka kama wasu miyagun.
Rundunar 'yan sanda ta samu gagarumar nasara a kan wasu 'yan ta'adda a jihar Anambra. An kama boma bomai 19 a maboyar yayin da aka harbi wasu da dama.
An yi kazamin fada tsakanin 'yan ssanda da 'yan bindiga a Katsina inda aka ceto mutum 10 amma biyu sun mutu. Rundunar ‘yan sanda tana cigaba da bincike kan lamarin.
Masu garkuwa da mutane sun kashe wani yaro dan shekara 10 Tasi’u Abdullahi a Filato duk da karbar kudin fansa. An rahoto cewa an gano gawarsa ne a cikin buhu.
Jami’an tsaro da ‘yan banga sun kashe “Al’jan,” dan ta’adda da ya addabi Tsafe, tare da kawo zaman lafiya ga mazauna yankin da ke fama da hare-hare.
Kwamandan hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) reshen jihar Kano, ya koka kan yawaitar hadurran motan da ake samu. Ya ce suna jawo asarar rayuka masu yawa.
Jami'an rundunar 'yan sandan jihar Imo, sun fafata da wasu 'yan bindiga da ake zargin na kungiyar IPOB ne. Jami'an tsaron sun hallaka mutum uku daga cikinsu.
Wasu 'yan bindiga da ake zargin suna da alaka da tantirin shugaban 'yan ta'adda, Bello Turji, sun yi garkuwa da wasu matafiya a jihar Sokoto da safiyar ranar Talata.
Yan bindiga
Samu kari