Yan bindiga
Dan majalisar tarayya a Amurka, Scott Perry, ya zargi hukumar USAID da taimaka wa kungiyoyin ta'adda, ciki har da Boko Haram da ke addabar Arewa maso Gabas.
Mazauna garin Maru a jihar Zamfara sun fito kan tituna domin nuna adawarsu kan karuwar hare-haren 'yan bindiga. Sun bukaci hukumomi su dauki mataki.
Gwamnonin Kudu maso Yamma sun kafa tawagar hadin gwiwa ta tsaro tare da amfani da fasahar zamani don tabbatar da tsaro da bunkasa tattalin arzikin yankin.
Jami'an rundunar 'yan sandan jihar Katsina sun samu nasarar dakile wani harin 'yan bindiga. Jami'an tsaron sun ragargaji 'yan bindigan tare da ceto mutane.
Gwamnatin tarayya da hadin gwiwar gwamnatin Zamfara sun kaddamar da shirin sauya tunanin 'yan bindiga a Arewa ta Yamma. Za a karbi 'yan ta'adda da suka tuba.
Wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun kai hare-haren ta'addanci a jihar Kaduna. 'Yan bindigan sun yi awon gaba da mutane masu yawa tare da kona gidaje.
Rahotanni sun tabbatar da cewa fitaccen shugaban 'yan bindiga, Kachalla Dan Lukuti, ya rasu bayan fama da wata muguwar cuta da ta sa ya fara yin haushin kare.
Rahotanni na ci gaba da fitowa kan yadda 'yan bindiga suka sace tsohon shugaban hukumar kula da masu yi wa kasa hidima (NYSC) Maharazu Tsiga a Katsina.
Gwamnatin jihar Zamfara karkashin jagorancin Gwamna Dauda Lawal ta sake bayyana matsayarta kan cewa ba za ta yi sulhu da 'yan bindiga masu kashe mutane ba.
Yan bindiga
Samu kari