Na Yafewa ‘Yan Ta’addan: Budurwar da Kwamandan Barayin Fasinjojin Jirgin Kasa Yaso Aure

Na Yafewa ‘Yan Ta’addan: Budurwar da Kwamandan Barayin Fasinjojin Jirgin Kasa Yaso Aure

  • Arzurfa Lois, budurwa mai shekaru 21 da kwamandan ‘yan ta’adda da suka sace fasinjojin jirgin kasa yaso aura tace ta yafe musu
  • Arzurfa tace kwamandan ya bukaci ta aure shi, ta zauna a wurinsa kuma zai sauya mata addini amma tace bata yarda ba, bai kuma tirsasa ta ba
  • Ta sanar da yadda suka yi kwanaki hudu suna tafiya a daji bayan sacesu da aka yi kafin su kai sansanin ‘yan ta’addan

Kaduna - Lois Azurfa, budurwa mai shekaru 21 da kwamandan ‘yan ta’addan da suka sace fasinjojin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna ya so aura, ta bayyana irin ukubar da ta sha yayin da take hannun ‘yan ta’adda.

Lois Arzurfa
Na Yafewa ‘Yan Ta’addan: Budurwar da Kwamandan Barayin Fasinjojin Jirgin Kasa Yaso Aure. Hoto daga punching.com
Asali: UGC

“Tabbas, da gaske ne kwamanda ya so aurena.”

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

- Arzurfa wacce ke cikin ragowar fasinjoji 23 da aka saki ranar Laraba da ta gabata ta sanar da manema labarai yayin da take gadon asibiti.

Ta kara da cewa ta yafewa ‘yan ta’addan da suka azabtar da su tun bayan da suka sace su a ranar 28 ga watan Maris a farmakin da suka kai wa jirgin kasa.

Jaridar Punch ta rahoto cewa, a yayin bayyana irin azabar da ta sha, dalibar aji uku ta jami’ar jihar Kadunan tace:

“Tun daga wurin kai harin, na ga jirgin kasan yayi tsayawar ba-zata kuma ‘yan ta’addan sun shigo tare da harbe-harbe sannan suka tasa keyarmu. Sun daure mazan tare da kwace wayoyinmu.
“Mun yi doguwar tafiya a wannan dare kafin babura su zo. Daga nan sun kai mu wani wuri inda muka kwana. Mun yi tafiyar kwanaki hudu kafin su kai mu asalin sansaninsu. Muna wurin babu abinda muke yi.”

Tace a duk lokacin da wadanda aka yi garkuwa dasu basu da lafiya, ‘yan ta’addan na kawo likitoci su duba su.

A yayin da aka tambayeta ko ‘yan ta’addan sun zabi wata sun ce suna son aurenta, Arzurfa tace:

“Eh, da gaske ne daya daga cikin kwamandojin ya zabe ni kuma yace yana son aurena. Amma bukata ce wacce nayi watsi da ita. Idan ka ki yadda basu tirsasa jama’a.
“Ba ni kadai bace ‘yan ta’addan suka so aure ba, zasu kawai tambayeki suna son aurenki. Suna son ajiyeki tare da sauya miki addini zuwa nasu. Ya rage naki ki yarda ko ki ki.”

Labarin barin sansanin ‘yan ta’addan yazo musu cike da mamaki don ‘yan ta’addan sun je tare da cewa su fara kwashe kayayyakinsu.

Zargin Sakin ‘Yan Boko Haram 101 daga Magarkamar Kirikiri Ya Tada Hankula

A wani labari na daban, a kalla mutum 101 da ake zargin ‘yan ta’addan Boko Haram ne ake zargin an saki daga gidan yarin Kirikiri dake jihar Legas, jaridar Punch ta rahoto hakan.

Kamar yadda shafin yanar gizo na gidauniyar jaridancin bincike ya bayyana, ma’aikatan gidan yarin sun bude musu hanya tare da sakinsu suka kama gabansu duk daga cikin yarjejeniyar sakin sauran fasinjojin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna wadanda aka sace a ranar 28 ga watan Maris.

Asali: Legit.ng

Online view pixel