'Yan Bindiga Sun Saki Sabon Bidiyo, Sun Ba 'Ya'yan Tsohon Akantan Zamfara da Suka Sace Bindiga

'Yan Bindiga Sun Saki Sabon Bidiyo, Sun Ba 'Ya'yan Tsohon Akantan Zamfara da Suka Sace Bindiga

  • 'Yan bindiga sun saki wani bidiyo mai ban mamaki kuma mai ban tsoro na yadda suka ba 'yan mata bindiga
  • 'Yan bindiga sun sace 'ya'yan tsohon akantan jihar Zamfara, sun shafe kwanaki 128 a hannun 'yan ta'adda
  • Bidiyon da muka samo ya nuna cewa, 'yan ta'addan suna barazanar da su auri 'yan matan tare mai dasu 'yan ta'adda

Zamfara - 'Yan bindigan dake rike da 'ya'ya mata biyu na tsohon akanta janar na jihar Zamfara, Abubakar Bala Furfuri da wata 'yar mai aikin gidansa sun yi barazanar mai da 'yan matan cikinsu a matsayin 'yan ta'adda.

Wannan na zuwa ne a cikin wasni bidiyon da 'yan bindigan suka sake tare da nuna bacin rai bisa kin biyan kudin fansa da tsohon akantan ya yi bayan sace 'yan matan.

Kara karanta wannan

Rikici: An farmaki hadimin Ganduje a Kano, ya ce 'yan Kwankwasiyya ne suka sace wayarsa

'Yan bindiga na barazanar ba 'ya'yan tsohon akantan Zamfara makami
'Yan Bindiga Sun Saki Sabon Bidiyo, Sun Ba 'Ya'yan Tsohon Akantan Zamfara da Suka Sace Bindiga | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

A cikin bidiyon mai mintuna biyu da sakanni 39 da aka saki a jiya Litinin 10 ga watan Oktoba da safe, an ga lokacin da 'yan bindigan suka ba 'yan matan makamai tare da tursasa su wajen yin magana.

'Yan matan dai su ne Zulaihat da Zainab, sai daya daga cikinsu da ba a bayyana sunanta ba da wasu daban.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Rahoton jaridar Premium Times ya ce, 'yan matan sun shafe kwanaki 128 a hannun 'yan ta'addan tun bayan sace su a watan Yuni.

An ga 'yan mata da bindiga

Bidiyon dai ya fara ne a daidai lokacin da 'yan ta'addan suka nuno 'yan matan rataye da bindigu tare da umartarsu da su bayyana gaskiyar su waye su da kuma kiran da suke wa iyayensu.

An gansu rataye da bindiga AK-47, LMG da sauran muggan makamai da 'yan ta'addan ke barna dasu a yankunan Arewacin Najeriya.

Kara karanta wannan

Mata da Yara 30 Sun Yi Shahada, Sun Nutse a Ruwa Za Su Tserewa ‘Yan Bindiga

A cikin bidiyon, daya daga cikin 'yan matan ta yi magana, ta roki iyayen da su taimaka su kawo kudin fansa kana a sako su.

Ta kuma shaida cewa, 'yan ta'addan ba sa cutar dasu, amma dai akwai bukatar a sake su su koma ga danginsu.

Muna neman karin abokan cin mushe

A bangaren 'yan bindigan, daya daga cikinsu da yake zantawa da 'yan matan ya bayyana cewa, idan ba a kawo kudin fansa ba za su maishe da 'yan matan cikinsu.

Ya ce tuni za a basu makamai tare da shigowa neman duk da masu kudi suke kana su tabbatar da aikata duk wani barna tunda 'yan matan sun san gidajen duk wani mai hali.

Hakazalika, ya ce idan iyayen basu kawo kudin fansa ba, tabbas zai aurar dasu a cikin 'yan bindigan tare da tursasa musu zama tare dasu.

Kalli bidiyon:

Gobara Ta Kama Majalisar Dokokin Jihar Kogi a Yau Litinin

Kara karanta wannan

Bacin rana: Wasu mutane sun fusata, sun raba dan luwadi da gangan jikinsa

A wani labarin, zauruka da farfajiyar majalisar dokokin jihar Kogi sun kama da wata gobara, inji wani rahoton Daily Trust.

Ya zuwa yanzu dai ba a san sanadiyyar kamawar wannan mummunan gobara ba da ta tashi a yau Litinin 10 ga watan Oktoba.

Kakakin majalisar dokokin jihar, Prince Mathew Kolawole ya shaidawa manema labarai cewa, hukumomi za su binciki lamarin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel